Duk Shan Wahala a Zaɓen Osun, Davido Ya Faɗi yadda Tinubu Zai Yi Nasara a 2027

Duk Shan Wahala a Zaɓen Osun, Davido Ya Faɗi yadda Tinubu Zai Yi Nasara a 2027

  • Mawaki a Najeriya, David Adeleke ya ce zai iya yin caca da kuɗinsa kan sake zaɓen Bola Tinubu a 2027, saboda rarrabuwar kawunan ‘yan adawa
  • Mawaƙin da aka fi sani da Davido ya ce kusan mutane takwas daga Kudu na son zama shugaban ƙasa, abin da ke hana ‘yan adawa haɗa kai
  • Davido ya ce nasarar Adeleke a Osun ta nuna akwai fata, amma ya bayyana siyasar Najeriya a matsayin mugunta, yana son nisantar cikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Shahararren mawaƙin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi magana kan zaben shugaban kasa a 2027.

Davoido ya ce zai iya yin caca da kuɗinsa kan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Davido ya magantu kan zaben Tinubu a 2027
Mawaki Davido da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Asiwjau Bola Tinubu, Davido.
Source: Instagram

Davido ya bayyana hakan ne yayin wata hira da News Central ranar Talata, inda yake magana kan yanayin siyasar Najeriya da kuma zaɓen gwamnan Osun da aka kammala.

Kara karanta wannan

Yan majalisa, kungiya sun taru kan Tinubu, sun shirya kifar da shi a mulki

Abin da ya tarwatsa yan adawa

A cewarsa, ‘yan siyasa da dama daga Kudu sun riga sun nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa, lamarin da ke sa ‘yan adawa kasa gabatar da haɗin kai wajen ƙalubalantar Tinubu.

Ya tambayi dalilin da ya sa ‘yan siyasar ba za su iya zama wuri ɗaya su yi aiki domin cimma manufa ɗaya ba, yana mai cewa haɗa kan ‘yan adawa zai iya haifar da babbar matsala ga shugaban ƙasa.

Davido ya ce sauya wannan yanayi zai buƙaci ƙoƙari sosai, amma ya ƙara da cewa sakamakon zaɓen gwamnan Osun da aka kammala ya nuna cewa har yanzu akwai fata.

Ya ce:

“’Yan adawa a Najeriya yanzu, idan za su ce, ‘To David, ka sanya kuɗinka, wannan ne zan yanke shawara a kai.’ Ba wai, ‘Oh, ba na son shiga zaɓen shugaban ƙasa ba ne.’ Zan iya cewa, ‘To, ina ganin shugaban ƙasa zai iya samun nasara cikin sauƙi,’ saboda ‘yan adawa sun rabu.

Kara karanta wannan

'Ba mu ga dama ba ne': Wike ya faɗi abin da za su yi da Tinubu su kwace Osun

“A Kudu kaɗai, kusan mutane takwas suna son zama shugaban ƙasa. Me ya sa ba za ku zauna tare ku tattauna ba? Domin bari in gaya muku, da akwai haɗaɗɗiyar ‘yan adawa, shugabanni na iya fuskantar babbar matsala. Amma ba su haɗu ba.
“Saboda haka, zai ɗauki abubuwa da yawa. Amma abin da ya faru a Osun ya nuna har yanzu akwai fata. Duk matasan Najeriya su ne makoma, kuma yanzu su ne ke da alhakin tafiyar da ƙasar.”

Davido ya nesanta kansa da siyasar Najeriya

A baya, mawaƙin ya nisanta kansa daga siyasar Najeriya, yana mai cewa ba ya sha’awar shiga tsarin siyasar ƙasar, wanda ya bayyana a matsayin “mugunta”.

Davido ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a X, yayin da yake mayar da martani ga masu sukar goyon bayan da ya bai wa kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke, a zaɓen gwamnan Osun da aka kammala.

An kaure da fada tsakanin Davido, dan majalisa

Mun ba ku labarin cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ikeja a Legas, James Faleke, ya musanta yunkurin yin tasiri kan INEC domin sauya sakamakon zaben gwamnan Osun.

Kara karanta wannan

Kasar Birtaniya ta aiko saƙo Najeriya bayan APC ta sha kaye a zaben gwamnan jihar Osun

James Faleke ya ce ya je Osun ne domin mara wa dan takarar APC, Bola Oyebamiji, baya, yayin da Davido ya goyi bayan kawunsa, Ademola Adeleke.

Gwamna Ademola Adeleke dai ya lashe zaben gwamnan Osun da kuri’u 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu 444,815.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.