Abubuwa 10 da Tinubu Ya Tabo a Jawabin Ranar Bikin Murnar Samun ‘Yancin Kai
- Bola Tinubu ya ce Najeriya ta tsallake mawuyacin halin da take ciki bayan sauye-sauyen tattalin arziki
- Muhimman ayyukan da ke gaban gwamnati sun hada da bunkasa harkar noma don rage tsadar rayuwa
- A jawabinsa na ranar 1 ga watan Oktoba, Tinubu ya bayyana nasarar da aka samu wajen inganta tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya yi wa al’ummar Najeriya jawabi da kasar ta ke bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai.
Jawabin cike yake da bayanin kalubale, nasarorin da gwamnati mai-ci ta samu a shekaru uku da kuma inda aka sa gaba.

Source: Facebook
Jawabin Shugaban kasa na ranar samun 'yancin-kai
Bayo Onanuga ya fitar da cikakken jawabin a shafinsa na X a safiyar Alhamis.
Gidajen jaridu sun duba wannan jawabi, suka tsakuro manyan bangarorin da ake ganin sun fi daukar hankalin jama’a a Najeriya.
Bisa al’ada, shugaban kasa yakan yi magana a rana irin ta yau - 1 ga watan Oktoba duk shekara.
Muhimman batutuwan da Bola Tinubu ya yi magana kai
1. An wuce bahar maliya
Leadership ta kawo wannan gaba a matsayin ta farko cikin jawabin da Mai girma Bola Tinubu ya yi a yau da safe.
Ya ce a fannin tattalin arziki, za a iya cewa an tsallake bahar maliya domin kuwa an gina dubalin farfado da kasar.
2. Gyare-gyare sun haifi ‘da mai ido
Shugaban na Najeriya ya ce a sakamakon sauye-sauyen da ya kawo, za a iya cewa an fara ganin nasara bayan shekaru uku.
Ya ce yanzu ana kokari ne wajen cin moriyar ribar da aka samu, an wuce matakin gyara kura-kuren da aka yi wa tattali.
3. Kare manufofin da ya kawo
Jawabin ya yi bayanin hikimar daukar wasu matakai da aka yi lokacin da sabuwar gwamnati ta shiga ofis a Mayun 2023.
Tinubu ya dage wajen rokon a yi watsi da masu kira da a maida hannun agogo baya a gyaran tattalin arzikin da yake yi.
4. Alkaluman tattalin arziki sun yi gaba
An kara fahimtar cewa tattalin arziki ya bunkasa da 4% bana sannan an samu raguwar masu satar danyen mai a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya ce hauhawar farashin kaya ya yi sauki kuma an ga yadda asusun kudin kasar wajen Najeriya ya tumbatsa.
5. Rage tsadar rayuwa
An rahoto shugaban yana cewa yanzu babu abin da ya sa a gaba irin ganin an samu sauki wajen tsadar rayuwa a fadin kasar.
Gwamnati tana so ta rage kudin sufuri tare da zamantar da harkar gona. Ana so kuma a gyara tituna, a farfado da layin dogo.
6. Samar da ayyuka
Ba a noma kadai ba, gwamnatin APC ta ci burin ganin matasa sun samu abin yi ganin Najeriya tana da arziki mai da gas.
Za a so a farfado da kamfanoni jkuma a kara koya wa mutane sana’o’i har ta kai ana fitar da kayan Najeriya zuwa ketare.
7. Rage talauci
Tinubu ya gamsu cewa miliyoyin mutane suna fama da abin da za su ci ko kudin abinci zuwa yadda za a biya kudin karatu.
Saboda haka ne ya ce gwamnatinsa ta ke kokarin tallafa wa irin wadannan iyaalai kai-tsaye a tsarin taimakon marasa galihu.
8. Sha’anin ilmi da kiwon lafiya
Ganin an janye tallafin mai, shugaban kasar ya ce za su cigaba da bunkasa harkar kiwon lafiya, ilmi da abubuwan more rayuwa.
An ji cewa Gwamnatin tarayya za ta cin ma nasara ne ta hanyar hada-kai da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi.
9. Dole Najeriya ta kara habaka
Shugaban Najeriya ya ce akwai bukatar matasa su zama silar karfin tattalin arziki ta hanyar samun damar sana’a da abin yi.
Yake cewa yana son ganin Najeriya ta kara habaka samar da kayayyaki da ayyuka a duniya da damammaki ga yara a gida.
10. Amanna da Renewed Hope
A karshen jawabin nasa, shugaban kasa ya yi kira ga dinbin ‘yan Najeriya su kara imani da manufarsa a kasar ta Renewed Hope.
Ya kammala da cewa ana daf da kai ga ci don haka a kara hakuri domin cin moriyar wahala da sadaukawar shekarun da aka yi.
Tinubu ya kara jaddada korar tallafin mai
Rahoto ya ce Gwamnatin Tarayya karkashin Jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta sanar cewa ba za ta dawo da tsarin tallafin man fetur ba.
Sakataren Gwamnati, George Akume, ya bayyana cewa cire tallafin da sauran tsare-tsare sun zama dole domin ceto tattalin arzikin kasa.
Bugu da kari, ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya samu bunƙasa da 4.2% a farkon shekarar 2026 sakamakon sauye-sauyen nan.
Asali: Legit.ng



