Zance Ya Kare: Shugaba Tinubu Ya Sanar da 'Yan Najeriya Halin da Ya Tsinci Kasar a 2023
- Bola Tinubu ya kwatanta Najeriya ta 2023 da mara lafiyar kansa da ke bukatar magani mai wahala domin samun damar murmurewa
- Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa sun tunkari matsalolin da suka dade suna addabar tattalin arzikin Najeriya
- Tinubu ya ce Najeriya ta kai wani mataki na sauyi, kuma gwamnati yanzu ta mayar da hankali kan samar da wadata ga jama’a baki ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kwatanta halin da ƙasar ke ciki a shekarar 2023.
Tinubu ya kwantanta halin da Najeriya ke ciki a 2023 da mara lafiyar da aka gano yana fama da cutar daji, wanda ke bukatar magani mai wahala domin samun damar rayuwa.

Source: Twitter
Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya yi wa ’yan Najeriya ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2026 domin bikin Ranar ’Yancin Kai. Bayo Onanuga ya sanya jawabin a shafinsa na X.
Tinubu ya yi maganar sauye-sauye
Shugaban kasar ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa sun zama dole domin gyara matsalolin da suka dade suna durƙusar da ƙasar. Tinubu ya ce dole a dauki mataki
Shugaban ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun tunkari wasu daga cikin tsofaffin matsalolin tattalin arzikin Najeriya.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin muhimman alamomin tattalin arziki sun fara samun sauƙi, lamarin da ya ce yana nuna cewa ƙasar na kan hanyar farfaɗowa.
A cewarsa, gwamnatin ta riga ta wuce matakin da ya kira “maganin gaggawa”, kuma yanzu ta mayar da hankali wajen samar da wadata ga ’yan Najeriya.
“A shekarar 2023, talauci na ƙaruwa, kuma fata ya kusa ƙarewa. Halin ƙasar ya fi duhu fiye da kowane lokaci. Ba mu da wani zaɓi illa mu ɗauki mataki.”
“Najeriya ta yi kama da mara lafiya”
Tinubu ya kwatanta Najeriya da mara lafiyar da aka sanar da cewa yana fama da cutar daji, inda likita ya bayyana masa cewa maganin zai kasance mai wahala da zafi, amma yana da kyakkyawar damar warkar da shi.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027
Ya ce mara lafiyar na da zaɓi biyu: ya fara magani, ya jure radadin da ke tattare da shi domin ya yaƙi cutar, ko kuma ya nemi maganin rage ciwo kawai, wanda zai rage radadin na ɗan lokaci yayin da cutar ke ci gaba da yaɗuwa.
“Na dogon lokaci, shugabannin Najeriya sun zaɓi abin rage zafin ciwo, suna addu’ar samun wata mu’ujiza da ba ta taɓa zuwa ba,” in ji shi.
Ya ce an yi watsi da matsalolin da suka dade
Tinubu ya ce gwamnatocin baya sun fi mayar da hankali kan alamomin matsalolin tattalin arziki maimakon magance tushensu. Ya ce an kashe makudan kuɗaɗe wajen ci gaba da wasu tsare-tsare marasa inganci waɗanda ba a tsara su da za su dawwama ba.
Ya ƙara da cewa lokacin da gwamnatinsa ta karɓi mulki, ta yanke shawarar sauya salon tafiyar da ƙasar.
“Mun zaɓi mu cire cutar daji. Sauye-sauyen da suka biyo baya sun kasance masu wahala. Illolinsu sun kasance a zahiri. Amma bai kamata mu taɓa rikita magani da cutar ba,” in ji Tinubu.
Tinubu ya kare sauye-sauyen da ya kawo
Shugaban ya jaddada cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta aiwatar ba su ne suka haifar da matsalolin tattalin arzikin ƙasar ba.
“Sauye-sauyenmu ba su haifar da raunin tattalin arzikinmu ba. Sun tunkare su ne.” In ji shi.

Source: Twitter
Gwamnatin Tinubu ba za ta dawo da tallafi ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za ta dawo da tsarin tallafin man fetur ba.
Ta bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar sun zama dole domin ceto ƙasar daga durƙushewa.
Asali: Legit.ng

