Yan Majalisa, Kungiya Sun Taru kan Tinubu, Sun Shirya Kifar da Shi a Mulki

Yan Majalisa, Kungiya Sun Taru kan Tinubu, Sun Shirya Kifar da Shi a Mulki

  • Ƙungiyar G100 ta gana da adawa ta Majalisar Wakilai, domin haɗa kan ‘yan adawa wajen kalubalantar Bola Tinubu a 2027
  • Shugaban G100 Salihu Lukman ya ce rarrabuwar jam’iyyun adawa na iya sake haifar da yanayin zaɓen 2023, wanda zai taimaka wa APC
  • Ƙungiyar ta ce ta tuntubi jam’iyyun ADC, NDC, PDP, APM, PRP da SDP, yayin da za a gudanar da taron adawa 31 ga Agusta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar G100 ta gudanar da wata muhimmiyar ganawa da yan adawa ta Majalisar Wakilai ta 10, a wani yunƙuri na haɗa kan ‘yan adawa.

Ganawar ta biyo bayan wata tattaunawa da ƙungiyoyin biyu suka yi a baya, inda aka mayar da hankali kan haɗa jam’iyyun adawa domin fuskantar APC a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Duk da shan wahala a zaɓen Osun, Davido ya faɗi yadda Tinubu zai yi nasara a 2027

Yan adawa na shirin kawo wa Tinubu cikas
Daya daga cikin yan adawa, Salihu Lukman da Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Shugaban tawagar G100 kuma tsohon Darakta-Janar na Progressive Governors’ Forum, Dakta Salihu Lukman na ADC, ya ce halin da ƙasa ke ciki ne ya haifar da wannan yunƙuri, cewar Punch.

Kuskuren da yan adawa suka yi a baya

Lukman ya ce rarrabuwar jam’iyyun adawa na iya sa su sake maimaita kuskuren zaɓen 2023, idan shugabanninsu ba su haɗa kai kafin 2027 ba.

A cewarsa, halin da Najeriya ke ciki ya sa ya zama dole shugabannin adawa su haɗa kai tare da samar da ingantaccen zaɓi ga masu kaɗa ƙuri’a.

Ya ce Najeriya ba za ta iya sake shafe wasu shekaru huɗu a ƙarƙashin gwamnatin APC ba, ya bayyana cewa G100 ta fara tattaunawa da shugabannin jam’iyyun siyasa shida, ciki har da ADC, New Nigeria Democratic Party (NDC), PDP, APM, PRP da SDP.

An shirya kifar da Tinubu a 2027
Shugaba Bola Tinubu ya yi tagumi a taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Shirin da jam'iyyun adawa ke yi

Dakta Lukman ya ce tawagar ta gana da ‘yan takarar shugaban ƙasa, mataimakansu da shugabannin ƙasa na waɗannan jam’iyyu, inda ta gabatar da shirin samar da haɗin kai kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

'Ba mu ga dama ba ne': Wike ya faɗi abin da za su yi da Tinubu su kwace Osun

Ya ce tattaunawar ta samu martani mai kyau daga mafi yawan shugabannin siyasa, sannan mataki na gaba shi ne gudanar da taron ƙasa na shugabannin adawa a ranar 31 ga Agusta.

An dage taron daga ranar da aka tsara shi tun farko domin ba da damar rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da kwamitin zaman lafiya na kasa.

Shugaban G100 ya roƙi Ƙungiyar Ƙananan Jam’iyyun Adawa da sauran masu ruwa da tsaki su mara wa shirin baya, yana mai cewa ƙungiyar ba ta son tafiya ita kaɗai.

Ya ce manufar ita ce haɗa ‘yan Najeriya da shugabannin siyasa masu sha’awar kayar da APC tare da samar da haɗin kai, cewar Tribune.

Har ila yau, ya kara da cewa G100 ta wuce adadin mutane 100 da suka sanya hannu kan sanarwar kafa ƙungiyar tun farko.

Wike ya yi alfahari kan zaben Osun

An ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce da Shugaba Bola Tinubu ya so APC ta lashe zaɓen Osun da ƙarfi, da ya taimaka masa, kuma Adeleke ba zai iya hana nasarar ba.

Wike ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta yi amfani da ƙarfinta wajen karkatar da zaɓen Osun ba, wanda Ademola Adeleke ya lashe.

Ministan ya yi hasashen cewa zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai fi sauƙi ga Tinubu saboda ya ce jam’iyyun adawa sun raunana sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.