Magana Ta Fito: An Ji Yadda Uwa da Diyarta Suka Mutu daga zuwa Karbo Tallafi a Wurin Gwamna

Magana Ta Fito: An Ji Yadda Uwa da Diyarta Suka Mutu daga zuwa Karbo Tallafi a Wurin Gwamna

  • MiBayanai na kara fitowa kan yadda wata mata da diyarta suka mutu a turmutsitsin da ya faru a Gidan Gwamnatin Jihar Neja
  • Wani ganau ya ce turmutsitsin ya biyo bayan jita-jitar cewa Gwamna Umaru Bago zai raba tallafin N10,000 ga mutane
  • Har yanzu babu tabbacin a hukumance kan adadin mutanen da suka mutu a lamarin da ya auku a gidan gwamnatin Neja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Sababbin bayanai sun fito kan yadda wata mata da diyarta suka mutu a turmutsitsin da ya faru a Gidan Gwamnatin Jihar Neja da ke Minna, yayin wani taron nuna goyon baya ga Gwamna Mohammed Umaru Bago.

Idan baku manta ba, Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu a gidan gwamnatin Neja a daren ranar Talata da ta gabata.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kashe wani shugaban jam'iyyar su Kwankwaso a Arewacin Najeriya

Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a fadar gwamnatinsa da ke Minna Hoto: Umaru Mohammed Bago
Source: Twitter

Asalin dalilin tarauwar jama'a

Wani ganau, Abu Zakeri, ya shaida wa Leadership cewa ba a shirya taron ba, illa dai taron nuna goyon baya ne da ya taso kwatsam ga gwamnan.

“Dukkanmu mun taru ne domin nuna goyon baya ga gwamnan, amma kwatsam sai muka ga wasu mata suna shigowa bayan sun ji cewa wai ana raba kuɗi a Gidan Gwamnati.
“A cikin wannan hali, gaba ɗayan harabar Gidan Gwamnatin ta cika da mutane, sai aka samu turmutsitsi. Kafin na bar wurin, mutane uku sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata aka kai su asibitin da ke cikin Gidan Gwamnatin,” in ji shi.

Abin da ya kai mata gidan gwamnatin Neja

Wata ganau, Maryam Ahmed, ta ce:

“Mun ji jita-jitar cewa ana raba kuɗi, sai muka yanke shawarar zuwa domin mu karɓi kuɗin. Amma lamarin ya rikice, kuma wasu mutane suka mutu.
“Ba zan iya cewa mutane nawa ne suka mutu ba saboda lokacin da lamarin ya rikice, wasu daga cikinmu muka bar wurin. Amma na san wata mata da diyarta da suka mutu."

Kara karanta wannan

An samu matsala, mutum 3 sun mutu a gidan gwammatin jihar Neja

Ta ce an birne matar da diyarta a makabartar Musulmi da ke Angwan Daji, inda ta ƙara da cewa mata na daga cikin waɗanda turmutsitsin ya fi shafa saboda ba su iya jure tsananin yanayin da aka shiga ba.

An ce lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, ya kai ziyara domin jajanta wa Gwamna Bago kan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37.

Yadda aka yada jita-jitar tallafin N10,000

Bayanai sun nuna cewa mutane sun taru ne bayan jita-jitar cewa gwamnan yana raba N10,000 ga kowane mutum a Gidan Gwamnatin tsakanin ƙarfe 7:00 na yamma zuwa 8:00 na dare ranar Talata.

An tattaro cewa lamarin ya ƙara rikicewa ne lokacin da gwamnan ya fito domin yi wa mutanen da suka taru jawabi, amma ya kasa samun hankalinsu, sannan ya koma cikin gidan.

Gwamna Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago da taron jama'a Hoto: Umaru Mohammed Bago
Source: Facebook

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, babu tabbacin hukuma kan adadin mutanen da suka mutu a lamarin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Da aka tuntubi Jami’in Hulɗa da Jama’a na ’Yan Sanda (PPRO), Wasiu Abiodun, ya ce ba shi da wani rahoto kan lamarin da ya faru a Gidan Gwamnatin.

Kara karanta wannan

Akwai alheri: An buɗe shirin da ake buƙatar matasa 'yan shekaru 15 zuwa 35 su cike a Najeriya

Yan bindiga sun sace manoma a Neja

Kun ji cewa ana zargin ’yan bindiga da yin garkuwa da manoma da dama a wasu hare-hare daban-daban a ƙaramar hukumar Mariga ta Jihar Niger.

Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Aliyu Bagga Muhamadu, ya ce adadin mutanen da aka sace ya kai 47, yana mai cewa masu garkuwar na neman N2m kan kowane mutum kafin su sake su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262