Latest
INEC ta yi hasashen adadin masu rajistar zaɓe a Najeriya zai haura miliyan 100 gabanin zaɓen 2027, yayin da hukumar ke shirin inganta wayar da kan masu zaɓe.
Mahaifin mawaki Davido, Adedeji Adeleke, ya fito fili ya bayyana cewa tsohon gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola,ya dage sai ya ga bayan Ademola Adeleke daga ofis.
Sojojin Iran sun gargadi kasashen Gulf da kada su taimaka wa sojojin Amurka a yakin da take yi, suna cewa hakan zai sa su zama masu hannu a hare-haren.
Hukumar INEC ta sanya 19 ga Satumba, 2026, domin gudanar da zaɓen cike gurbin Gombe/Kwami/Funakaye, bayan rasuwar ɗan majalisar yankin Yaya Bauchi Tongo.
A labarin nan, za a ji abubuwan da suka jawo jam'iyyar APC da gwamna Nasir Idris suka yanke sahwarar hakura da mataimakin gwamna a zaben 2027 mai zuwa.
Tsoffin sojojin Najeriya sun shirya zanga-zanga a Abuja kan rashin karin fansho, yayin da aka jibge jami’an tsaro a Ma’aikatar Tsaro da ke birnin tarayya.
Kotun Majistare ta Ekiti ta tsare tsohuwar ’yar takarar gwamnan APC, Abimbola Olajumoke, kan zargin bata suna, cin zarafin yanar gizo da satar mutane.
A wata hira da aka yi da shi, Ayo Fayose ya ce Peter Obi nagari ne amma ba shi da damar cin zaben 2027 saboda rabuwar kan 'yan hamayya mai hana nasara.
Hukumar INEC ta ce za ta tura kusan ma’aikatan wucin gadi miliyan 1.4 zuwa rumfunan zaɓe sama da 176,000 a faɗin Najeriya domin babban zaɓen 2027.
Masu zafi
Samu kari