Kasa Za Ta Yi Seti, Tinubu Ya Juyo kan Abin da Ya Fi Damun Yan Najeriya

Kasa Za Ta Yi Seti, Tinubu Ya Juyo kan Abin da Ya Fi Damun Yan Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bangaren da zai mayar da hankali domin sauƙaƙa rayuwar ’yan Najeriya
  • Tinubu ya ce gwamnati za ta rage kuɗin samar da kayayyaki da sufuri, tare da bunƙasa noma, masana’antu da ayyukan yi
  • Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arziki sun jawo wahala, amma gwamnati za ta ci gaba da su tare da ƙarfafa tallafin marasa galihu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa rage tsadar rayuwa shi ne babban fifikon gwamnatinsa a yanzu.

Bola Tinubu ya ce gwamnati za ta rage kuɗin samarwa da jigilar kayayyaki domin sauƙaƙa rayuwar ’yan Najeriya.

Tinubu ya kwantar wa yan kasa hankali
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yana jawabi a Abuja. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Twitter

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na Ranar ’Yancin Najeriya ranar Alhamis, yayin da ƙasar ta cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Tinubu ya sanar da 'yan Najeriya halin da ya tsinci kasar a 2023

Kokarin Tinubu a cikin shekaru 3

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shafe shekaru uku tana gyara tattalin arzikin ƙasar, kuma yanzu ta karkata hankali ga “wadatar da kowa.”

Shugaban ya ce:

“Babban fifikonmu shi ne rage tsadar rayuwa. Za mu cimma hakan ne ta hanyar rage kuɗin samar da abubuwan da ’yan Najeriya ke amfani da su da kuma jigilar su.”

Ya ce tsarin gwamnatin zai haɗa da faɗaɗa ban ruwa na zamani da noman rani, inganta samun iri da takin zamani, ƙara amfani da injinan noma, da saka hannun jari wajen ajiyar amfanin gona da sufuri.

‘Lokacin kawo sauyi na gaggawa ya ƙare’

Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya sun zama dole saboda ƙasar ta daɗe tana jinkirta yanke wasu matakai masu wahala, lamarin da ya sa matsalolin tattalin arziki suka ƙara ta’azzara.

Ya ce zuwa shekarar 2023, yanayin ya tsananta, inda a cewarsa talauci ke ƙaruwa, yayin da fata ta kusan gushewa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan maido tallafin mai a ranar 'yanci

Shugaban ya yi amfani da misalin mai fama da cutar daji wajen bayyana halin tattalin arzikin ƙasar, yana cewa gwamnatocin baya sun fi magance alamomin matsalar maimakon tushenta.

Shugaban ya ce gwamnati za ta yi watsi da kiraye-kirayen dakatar da sauye-sauyen tare da komawa abin da ya bayyana a matsayin “cin zarafin tallafin mai da ya zama abin dogaro.”

Tinubu ya yi alkawari ga yan Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Gwamnati za ta rage kuɗin abinci da sufuri

Shugaban ya ce mataki na gaba na gwamnatinsa zai mayar da hankali wajen tabbatar da cewa ci gaban tattalin arziki ya koma inganta yanayin rayuwar ’yan Najeriya.

Ya ce rage tsadar rayuwa zai buƙaci rage kuɗin samar da kayayyaki a noma, masana’antu da sufuri, Vanguard ta tabbatar da haka.

Tinubu ya magantu kan yadda ya samu Najeriya

A wani labarin, an ji cewa Bola Tinubu ya kwatanta Najeriya ta 2023 da mara lafiyar kansa da ke bukatar magani mai wahala domin samun damar murmurewa.

Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa sun tunkari matsalolin da suka dade suna addabar tattalin arzikin Najeriya.

Tinubu ya ce Najeriya ta kai wani mataki na sauyi, kuma gwamnati yanzu ta mayar da hankali kan samar da wadata ga jama’a baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.