An Jibge Jami'an Tsaro da Tsofaffin Sojoji Suka Barke da Zanga Zanga a Abuja

An Jibge Jami'an Tsaro da Tsofaffin Sojoji Suka Barke da Zanga Zanga a Abuja

  • An girke jami’an tsaro da dama a hedkwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja, gabanin zanga-zangar tsofaffin sojoji kan fansho
  • Tsofaffin sojojin sun ce karin albashin da aka yi wa jami’an da ke aiki ya kamata ya haifar da karin fansho ga masu ritaya
  • Shugabannin masu ritaya sun ce za su gudanar da zanga-zangar domin neman hakkokinsu na fansho, duk da tsauraran matakan tsaro a wurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An jibge jami’an tsaro da dama daga rundunar sojin Najeriya, ’yan sanda, Hukumar Shige da Fice da VIO a hedkwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja.

An ce an kara yawan jami’an tsaron ne domin tunkarar babbar zanga-zangar da tsofaffin sojoji suka shirya kan rashin aiwatar da karin fanshon da ya dace.

Tsofaffin sojoji sun fara zanga-zanga a Abuja
Taswirar birnin tarayya Abuja da tsofaffin sojoji suka fara zanga-zanga. Hoto: Legit.
Source: Original

Bukatar tsofaffin sojojin Najeriya

Kara karanta wannan

Sojoji sun ɗana tarko, an daƙile harin garkuwa da mutane a Zamfara

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsarin albashi ga jami’an sojin Najeriya domin kara inganta ayyukansu a wuraren da suke gudanar da aiki.

Karin albashin ya shafi dukkan matakan sojoji, amma tsoffin sojojin sun ce bai kamata a bar su a baya ba, bayan sun yi wa kasa hidima.

Lokacin da ƴan jarida suka ziyarci hedkwatar Ma’aikatar Tsaro da safiyar Laraba, an kirga akalla motocin yaki masu sulke guda uku mallakar sojoji.

Haka kuma, an ga sama da motoci 18 na ’yan sanda, sojoji, Shige da Fice, VIO, NSCDC, FRSC da sauran hukumomin tsaro.

An ga sojoji dauke da makamai suna sintiri a wajen, yayin da jami’an tsaro suka mamaye hanyoyin da suka isa ma’aikatar, lamarin da ya haddasa cunkoson ababen hawa.

Ko da yake zanga-zangar ba ta fara ba lokacin da aka gabatar da wannan rahoto da misalin karfe 9:10 na safe, tsofaffin sojojin sun ce ba za su fasa ba.

Wani tsohon soja, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce ya kamata ministan ya gana da su domin warware matsalar, amma mutanen da ke kusa da shi suka hana hakan.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sauya taku, an tura zazzafan gargadi ga 'yan ta'adda

Ya ce:

“Janar Christopher Musa mutum ne mai kirki. A kodayaushe yana son ganin an kula da jin dadin jami’an da ke aiki da wadanda suka yi ritaya, amma wadanda ke kusa da shi ba sa son ya yi nasara.
“Wannan zanga-zangar za ta gudana kamar yadda aka tsara domin jawo hankalin duniya cewa mu ma mun cancanci a yi mana adalci, ba danniya ba. Mu ma mun cancanci abin da aka bai wa jami’an da ke aiki.”
Tsofaffin sojoji sun nemi agajin ministan tsaro
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Musabbabin zanga-zangar tsofaffin sojoji

Ya bayyana cewa tsofaffin sojojin na zanga-zangar ne saboda zargin gazawar hukumomi wajen aiwatar da karin fansho sakamakon karin albashin jami’an soji da ke aiki.

Daya daga cikin shugabannin tsoffin sojojin, Kanar Innocent Azubike mai ritaya, ya ce zanga-zangar na neman abin da ya kira hakkokin fanshon da kundin tsarin mulki ya ba su.

Azubike ya ce Shugaba Bola Tinubu ya amince da karin albashi ga jami’an soji a watan Nuwamba 2025, wanda ya kamata ya haifar da karin fansho ga wadanda suka yi ritaya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

2027: Jigon APC ya fadi abubuwan da za su zama matsala ga Tinubu

Sai dai ya zargi hukumomi da kin aiwatar da karin, duk da cewa manyan jami’an soji sun sha tabbatar da amincewar shugaban kasa.

Azubike ya ce:

“Muna da zanga-zanga a Ma’aikatar Tsaro domin neman hakkokinmu na fansho da kundin tsarin mulki ya ba mu.
“A watan Nuwambar bara, Shugaban kasa ya amince da sabon karin albashi ga sojoji, kuma ya zo da karin da ya dace ga wadanda suka yi ritaya da masu karbar fansho.”

Gwamnatin Tinubu ta nemi tsofaffin sojoji

A baya, an ji cewa Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin tura tsofaffin sojoji domin kare wuraren da ba su samu cikakken tsaro ba.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya kafa kwamitin mutum 18 domin dawo da wadannan wurare.

Musa ya ce amfani da tsofaffin sojoji zai rage dogaro da farmakin soja kaɗai, ya ƙara sahihan bayanan sirri, tare da gina amincewa tsakanin al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.