Duk da Korafe Korafe, Tinubu Ya Bayyana Nasarorinsa a Fannin Tattalin Arziki

Duk da Korafe Korafe, Tinubu Ya Bayyana Nasarorinsa a Fannin Tattalin Arziki

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan sauye-sauyen tattalin arziki, bayan shekaru uku da rabi da gwamnatinsa ta fara gyare-gyare
  • Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya karu da sama da kashi huɗu cikin 2026, yayin da satar mai da hauhawar farashi suka ragu sosai
  • Tinubu ya ce lokacin gyaran tattalin arziki na gaggawa ya wuce, inda gwamnati yanzu za ta mayar da hankali kan samar da wadata ga jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayyana nasarorin tattalin arziki da ya ce ƙasar ta samu tun bayan da ya karɓi ragamar mulki shekaru uku.

Shugaba Tinubu ya ce tattalin arzikin ƙasar ya fara samun sauye-sauye wanda ya kawo ci gaba a fannoni da dama.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da Tinubu ya tabo a jawabin ranar bikin murnar samun ‘yancin kai

Tinubu ya tunawa yan Najeriya nasarorin da ya samu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Hakan na cikin jawabin da ya gabatar wa ’yan Najeriya domin bikin cikar ƙasar shekaru 66 da samun ’yancin kai da hadiminsa, Bayo Onanuga ya wallafa a X.

Yadda tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa

Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu ƙaruwa da sama da kashi huɗu cikin 2026, inda bangaren mai da wanda ba na mai ba suka taimaka wajen samun ci gaba.

Tinubu ya kuma ce an samu raguwar satar danyen mai, yayin da hauhawar farashi ta ragu sosai idan aka kwatanta da lokacin da ta kai kololuwa.

Ya ce an sake gina asusun ajiyar kuɗin waje na ƙasar, sannan kasuwar musayar kuɗaɗen waje ta samu daidaito fiye da yadda take a baya.

Shugaban ya ƙara da cewa Najeriya ta samu sama da dala biliyan shida daga fitar da kayayyakin da ba na mai ba zuwa ƙasashen waje a 2025.

Tinubu ya yi alkawura ga yan kasa
Shugaban kasar Najeriya a yayin wani taro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Yawan kudin da aka samu a Najeriya

Kara karanta wannan

Kasa za ta yi saiti, Tinubu ya juyo kan abin da ya fi damun yan Najeriya

A cewarsa, wannan shi ne mafi yawan kuɗin da Najeriya ta taɓa samu daga fitar da kayayyakin da ba na mai ba a tarihin ƙasar.

Ya ce:

“Waɗannan ba iƙirarin da ba su da tushe ba ne."

Ya ce kungiyoyin sa-kai da cibiyoyin ƙasa da ƙasa masu taimaka wa gwamnatoci ma sun lura da ƙarin daidaito da juriyar tattalin arzikin Najeriya.

Tinubu ya ce saboda haka babban burin tattalin arzikin gwamnatinsa ya sauya daga gyara tafarkin tattalin arzikin Najeriya zuwa samar da “wadata da kowa zai amfana da ita.”

Ya ce mataki na gaba zai mayar da hankali wajen ganin ci gaban tattalin arziki ya koma sauyi da ’yan Najeriya za su iya gani a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya lissafa samun abinci da araha da sufuri mai sauƙi, wutar lantarki mai inganci, damar samun rance da ayyukan yi masu amfani a matsayin abubuwan da za a fi mayar da hankali.

Tinubu zai saukaka wa yan Najeriya

Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana bangaren da zai mayar da hankali domin sauƙaƙa rayuwar ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Tinubu ya sanar da 'yan Najeriya halin da ya tsinci kasar a 2023

Tinubu ya ce gwamnati za ta rage kuɗin samar da kayayyaki da sufuri, tare da bunƙasa noma, masana’antu da ayyukan yi.

Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arziki sun jawo wahala, amma gwamnati za ta ci gaba da su tare da ƙarfafa tallafin marasa galihu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.