Tsugune ba Ta Ƙare ba: Iran Ta Ja Kunnen Saudiyya, Sauran Makwabta game da Amurka

Tsugune ba Ta Ƙare ba: Iran Ta Ja Kunnen Saudiyya, Sauran Makwabta game da Amurka

  • Rundunar sojin Iran ta gargadi ƙasashen da ke yankin Gulf da su guji taimaka wa sojojin Amurka a yankin
  • Shugaban hafsoshin soji, Ali Abdollahi, ya ce duk taimako da aka bai wa Amurka zai zama kamar shiga aikin sojin kasar ne
  • Iran ta ce tana sane da jiragen saman sojin Amurka da ke amfani da sansanonin yankin, yayin da USS George Washington ke komawa yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Rundunar sojin Iran ta gargadi ƙasashen yankin Gulf a ranar Laraba kan taimaka wa sojojin Amurka ta kowace hanya.

Rundunar sojojin Iran ta yi gargadin ne tana mai cewa hakan zai zama kamar shiga ayyukan sojin Amurka ne mai tsaye.

Iran ta sake gargadin kasashen Larabawa game da Amurka
Dan Sarkin Saudiyya, Muhammad Bn Salman da Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran. Hoto: Inside the Haramain, Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Gargadin Iran ga kasashen Larabawa

Shugaban hafsoshin sojin Iran, Ali Abdollahi ne ya bayyana haka inda ya yi wa kasashen barazana, cewar rahoton Anadolu Ajansi.

Kara karanta wannan

Iran ta dauko da zafi, ta gargadi makwabtanta kan taimakon Amurka

Abdullahi ya ce:

“Muna son gargadin cewa duk wani taimako ko sauƙaƙawa da aka bai wa sojojin Amurka masu kai hari, yana nufin shiga aikin sojin Amurka ne.”

Ya ce hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yaƙin da ya barke tsakanin Iran da Amurka tun ranar 28 ga Fabrairu, bayan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran.

Iran ta mayar da martani ga hare-haren da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa, ciki har da kai hare-hare kan sansanonin Amurka da ke yankin.

Abdollahi ya ce:

“Da wuya a samu irin wannan adadi mai yawa na jiragen saman soja, musamman jiragen da ke ɗaukar mai, a sansanonin yankin ba tare da ƙasashen da ke karɓarsu sun sani ba.
“Ƙasashen da ke makwabtaka da Tekun Farisa, waɗanda suka bayyana cewa ba za su bari Amurka ta yi amfani da yankunansu wajen kai wa Iran hari ba, ya kamata su san cewa muna sane da halin da ake ciki.”

Kara karanta wannan

An jibge jami'an tsaro da tsofaffin sojoji suka barke da zanga zanga a Abuja

Iran ta sha alwashi kan masu taimakawa Amurka
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Amurka na shirin sauya jirgin yakin ruwanta

Gargadin Iran ya zo ne yayin da ake shirin mayar da jirgin ruwan yaƙin Amurka USS George Washington zuwa Gabas ta Tsakiya domin maye gurbin USS Abraham Lincoln.

Rahotanni sun ce ana mayar da USS George Washington yankin ne bayan samun rahotannin cewa yanayin rayuwar ma’aikatan USS Abraham Lincoln ya tabarbare, cewar Punch.

Yakin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka ya kara tsami ne tun bayan barin ranar 28 ga watan Fabrairun 2026 wanda ya yi ajalin manyan jami'an tsaron Iran ciki har da Ali Khamenei.

Amurka, Saudiyya sun farmaki masoyan Iran

An ji cewa Amurka da Saudiyya sun kai hare-hare kan kungiyoyin da Iran ke marawa baya a Iraki bayan hare-haren jiragen sama marasa matuki.

Saudiyya ta ce jiragen kariyarta sun kakkabo jirage marasa matuki, tana zargin mayakan da Iran ke goyon baya da kai hare-haren daga cikin Iraki.

Kasashen biyu sun ce ba sa neman rikici, amma sun jaddada cewa za su kare kasashensu da kadarorinsu idan aka sake kai musu hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.