Jirgin Sama Dauke da Hamshakin Attajiri Ya Rikito, Matarsa da Sauran Mutane Sun Mutu

Jirgin Sama Dauke da Hamshakin Attajiri Ya Rikito, Matarsa da Sauran Mutane Sun Mutu

  • Attajirin Zimbabwe Wicknell Chivayo da matarsa Lucy Muteke sun mutu bayan jirgin sama mai saukar ungulu da suke ciki ya yi hatsari
  • Jirgin ya yi hatsarin ne a yankin karkara na Marondera, mai tazarar kusan kilomita 70 daga gabashin Harare, babban birnin Zimbabwe
  • Jami’an gwamnati sun ce mutane shida ne ke cikin jirgin, kuma babu wanda ya tsira, yayin da bincike kan musabbabin hatsarin ke ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Harare, Zimbabwe - Attajirin Zimbabwe kuma ɗan kasuwa, Wicknell Chivayo, da matarsa Lucy Muteke, sun mutu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu da ya yi sanadin mutuwar mutane shida.

Jirgin ya yi hatsarin ne a yankin karkara na Marondera, mai tazarar kusan kilomita 70 daga gabashin Harare, babban birnin Zimbabwe, a yammacin Laraba, 30 ha watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027

Dan kasuwa ya mutu a hatsarin jirgi
Hamshakin dan kasuwa, Chivayo Hoto: sirwicknell
Source: Instagram

Mutane shida na cikin jirgin

A cewar tashar BBC, ’yan sandan Zimbabwe sun ce mutane shida ne ke cikin jirgin, wanda ya yi hatsarin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma agogon ƙasar.

Daga bisani jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa babu wanda ya tsira daga hatsarin.

Herbert Chivayo, mai magana da yawun iyalan marigayin, ya tabbatar da rasuwar ɗan kasuwar da matarsa ga gidan rediyon ƙasar Zimbabwe, ZBC.

“Mun rasa abin cewa bayan samun wannan mummunan labari,” in ji shi.

Jirgin ya yi hatsari bayan mintuna 40 da tashinsa

A cewar ZBC, ma’auratan suna kan hanyarsu ne daga Gandami, a Chikomba, inda suke gina wani gida a karkara.

Rahoton ya ce jirgin ya yi hatsarin ne a Kudenga Farm, kimanin mintuna 40 bayan tashinsa.

Har yanzu ba a bayyana musabbabin hatsarin ba, yayin da ’yan sanda suka ce sun fara bincike domin gano abin da ya haddasa shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tattara manoma kusan 50 zuwa daji, sun nemi makudan kudin fansa

Jami’ai sun tabbatar da babu wanda ya tsira

Kakakin gwamnatin Zimbabwe, Nick Mangwana, ya tabbatar da faruwar hatsarin, yana mai cewa jirgin na ɗauke da “fitaccen ɗan kasuwa, wasu fasinjoji uku da matukan jirgi biyu”.

“Bayanan da muke da su a yanzu sun nuna cewa babu wanda ya tsira daga wannan hatsari,” Mangwana ya rubuta a shafinsa na X.

Wanene Wicknell Chivayo?

Chivayo shi ne manajan darakta na Intratrek Zimbabwe, kuma ya shahara sosai saboda rayuwar alfarma da yake nunawa, ayyukan tallafa wa jama’a da kuma alaƙarsa da manyan mutane a faɗin Afirka.

Ɗaya daga cikin manyan ayyukan kasuwancinsa shi ne wani aikin samar da wutar lantarki daga hasken rana da darajarsa ta kai dala miliyan 172 a Gwanda.

Kamfanin Intratrek ne gwamnatin Zimbabwe ta ba aikin ta hannun kamfanin wutar lantarki mallakar gwamnati, Zimbabwe Power Company. Daga bisani aikin ya shiga cikin takaddamar shari’a da ta ɗauki shekaru.

An taɓa bincikarsa kan kwangilolin zaɓe

Chivayo ya kuma fuskanci bincike kan sayen kayayyakin da aka yi amfani da su a zaɓen Zimbabwe na 2023, wanda ya kasance cikin ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Shugaban APC ya hango matsalar da Arewa za ta shiga idan Tinubu bai zarce ba

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar ta binciki zarge-zargen da suka shafi kwangilolin da aka bai wa wani kamfanin Afirka ta Kudu mai suna Ren-Form.

Sai dai hukumar ta rufe binciken a shekarar 2025, tana mai cewa ba ta gano wata hujja da ke danganta Chivayo ko Hukumar Zaɓe ta Zimbabwe da aikata ba daidai ba.

Ya shahara da kyautata wa fitattun mutane

Chivayo ya kuma yi fice wajen bai wa mawaka, shugabannin addini da sauran fitattun mutane motoci na alfarma da makudan kuɗaɗe, inda ake yawan wallafa irin waɗannan kyaututtuka a shafukan sada zumunta.

Alaƙarsa da manyan mutane ba ta tsaya a Zimbabwe ba.

Ya gana da shugabannin kasashe a Afirka

Chivayo ya kasance yana yawan wallafa hotunansa tare da shugabannin ƙasashen Afirka.

Daga cikin shugabannin da ya taɓa wallafa hotunansa tare da su akwai shugaban Zambia Hakainde Hichilema, shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, shugaban Tanzania Samia Suluhu Hassan, da Sarkin Eswatini Mswati III.

Hukumomin Zimbabwe na ci gaba da bincike domin gano ainihin musabbabin hatsarin da kuma tabbatar da cikakkun bayanan sauran mutanen da suka mutu a lamarin.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da sabon rikici ya barke a Taraba, rayuka sun salwanta

Wicknell Chivayo ya mutu
Wicknell Chivayo wanda ya rasu a hatsarin jirgi Hoto: sirwicknell
Source: Instagram

Jarumin fim ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa masana’antar fina-finan Najeriya ta shiga jimami bayan rasuwar ɗan wasan Nollywood, Chijioke “Cjay” Nwokafor.

Jarumin na masana'antar Nollywood ya yi bankwana da duniya ne a ranar Laraba, 30 ga watan Satumban 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng