Nasara: An Kama Wanda Ya Shirya Harin da Aka Shiga Gida Gida Ana Yanka Mutane a Najeriya

Nasara: An Kama Wanda Ya Shirya Harin da Aka Shiga Gida Gida Ana Yanka Mutane a Najeriya

  • Dakarun Rundunar 'Yan sanda sun kama babban wanda ake zargi da hannu a harin da ya yi ajalin mutane 25 a yankin Mangu ta jihar Filato
  • Sojoji sun ƙaddamar da Operation Hard Nut tare da tura ƙarin dakaru domin farautar maharan a yankin da lamarin ya auku
  • Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da bincike kan wanda aka kama da kuma kokarin cafke duk wani mai hannu a harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau, Nigeria - Rundunar ’yan sanda a Jihar Plateau ta kama babban wanda ake zargi da hannu a harin da aka kai kauyen Bimper da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a safiyar Talata.

Mutane 25 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu huɗu suka jikkata a harin wanda aka ce maharan sun rika shiga gida-gida suna yanka mutane.

Kara karanta wannan

Saurayi ya yi jima'i da budurwa, ya fille mata wuya ta mutu ya sha jinin ta a otel

Yan sanda.
Dakarun yan sanda a cikin motar sintiri lokacin da duka fito aiki a Najeriya Hoto: PoliceNG
Source: Twitter

An kama wanda ya kitsa harin Mangu

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Alfred Alabo, ya tabbatar wa Channels TV da kama wanda ake zargin, inda ya ce ana kyautata zaton shi ne ya shirya harin.

Ya ƙara da cewa bincike na ci gaba, yayin da rundunar yan sanda ke ci gaba da farautar sauran maharan da suka tsere.

Harin ya faru ne da sanyin safiyar Talata, inda ya zama hari na uku da aka kai a Mangu cikin mako guda.

Sabon harin ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin, waɗanda ke kira ga gwamnati da ta ƙara tsaurara matakan tsaro tare da kare al’ummomi daga ƙarin hare-hare.

Sojoji sun kaddamar da Operation Hard Nut

Kwamandan Runduna ta 3 ta Sojojin Najeriya, Manjo Janar Maxwell Dangana, ya mayar da ofishinsa na dabarun yaƙi zuwa Ƙaramar Hukumar Mangu na tsawon makonni biyu.

Hakan na zuwa ne yayin da dakarun sojojin suka ƙaddamar da Operation Hard Nut domin fatattakar ’yan ta’adda da dawo da zaman lafiya bayan harin da aka kai wa al’ummar Bimper.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ɗana tarko, an daƙile harin garkuwa da mutane a Zamfara

Dangana ya ba da umarnin ne yayin da yake jawabi ga sojoji a hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mangu a lokacin wani atisayen nuna ƙarfi, jim kaɗan bayan harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 25.

Sojoji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @NigerianArmy
Source: Twitter

GOC ɗin ya umarci sojojin da su kasance masu ƙwarewa da kuma tsaka-tsaki wajen gudanar da ayyukansu.

Ya ce Operation Hard Nut za ta mayar da hankali wajen kawar da dukkan ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka da ke aiki a Mangu, tare da dawo da kwarin gwiwar mazauna yankin da hare-hare suka addaba.

Janar Dangana ya bayyana cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa ya amince da tura ƙarin dakaru da kayan aiki domin tallafa wa aikin.

Yan sanda sun kama fasto da sojoji

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ’yan sandan Jihar Plateau ta kama wani fasto da jami’an tsaro biyu kan zargin shirya satar matan manyan limamai biyu a Jos.

Rundunar ta bayyana daya daga cikin wadanda ake zargin da sunan Rev. Hassan Yunisim Mijah, mai shekaru 42, mazaunin Tudun Wada da ke Jos ta Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262