Asibitin India Ya Yi Talla da Hotunan Kashim Shettima, Abdulsalami Abubakar

Asibitin India Ya Yi Talla da Hotunan Kashim Shettima, Abdulsalami Abubakar

  • Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ya bayyana a tallan wani asibitin Indiya bayan da aka yi masa tiyata
  • Asibitin Krishna Shalby da ke Ahmedabad ya wallafa hotunan Abubakar da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima
  • Dokar Najeriya ta bai wa tsofaffin shugabannin ƙasa da iyalansu damar samun magani a Najeriya ko ƙasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An yi amfani da hoton tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, a wani tallan asibitin Indiya bayan da aka yi masa tiyatar gwiwa a ƙasar.

Wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya nuna Abubakar yana samun kulawa a asibitin Krishna Shalby da ke Ahmedabad, India, ciki har da yadda yake tafiya da motsa jiki bayan tiyatar.

Asibitin India ya yi talla da hotunan Shettima, Abdulsalami
Tsohon shugaban mulkin soja, Abdulsalami Abubakar da Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Facebook

Asibitin ya kuma yi amfani da hotunan tsohon shugaban ƙasar da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a wasu wallafe-wallafen da ke tallata ayyukansa ga marasa lafiya daga ƙasashen duniya, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Hutu ya kare: Shugaba Tinubu ya bar Faransa, ba zai sauka a Abuja ba idan ya dawo Najeriya

Abin da ya kai Shettima asibitin India

Asibitin ya wallafa ya ce Kashim Shettima ya ziyarci asibitin tare da ganawa da tattauna halin da Abubakar ke ciki da lafiyarsa.

Asibitin ya bayyana ziyarar a matsayin alamar “ƙara samun amincewa da harkokin kiwon lafiya a Indiya” da kuma ƙudurinsa na kula da marasa lafiya daga sassa daban-daban na duniya.

Sanarwar ta ce:

“Lokacin da marasa lafiya suka ketare iyakoki domin samun kulawa ta musamman, amincewarsu ita ce komai."

Ba a bayyana nan take ko Gwamnatin Tarayya ce ta ɗauki dukkan kuɗin jinyar Abubakar ba.

Dokar ta kuma tanadi wasu alawus-alawus, ciki har da fasfo na diflomasiyya, gata na musamman, motocin gwamnati, ofis da gidajen zama, tsaro da kuma hutun shekara-shekara da Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki nauyinsu.

A cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 2.3 domin biyan hakkokin tsofaffin shugabannin ƙasa, shugabannin soja da mataimakansu.

Kara karanta wannan

2027: Kalubalen da ke gaban Akpabio, Barau Jibrin da shugabannin majalisa

Kashim Shettima ya ziyarci asibitin India
Mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Twitter

Martanin ’yan Najeriya kan jinya a ketare

Amfani da jinyar Abdulsalami Abubakar wajen tallan asibitin ya jawo martani daga wasu ’yan Najeriya.

Mai fafutuka kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, na cikin waɗanda suka mayar da martani bayan ya wallafa bidiyon tallan a shafinsa na X ranar Talata.

Ya ce:

“Wannan shi ne tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, wanda aka yi amfani da shi a tallan asibiti bayan an yi masa tiyatar maye gurbin gwiwa a Indiya."

Ya tambayi dalilin da ya sa shugabannin Najeriya, waɗanda suka samu damar inganta tsarin kiwon lafiya a lokacin da suke mulki, ke ci gaba da zuwa ƙasashen waje domin samun kulawa ta musamman.

Tinubu ya tura Shettima taron UNGA

Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya tura Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya duro Najeriya yayin da ake jiran dawowar Tinubu

Shettima zai jagoranci tawagar Najeriya da ta ƙunshi gwamnoni, ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati zuwa birnin New York.

Babban taron na Majalisar Ɗinkin Duniya zai gudana daga ranar 22 zuwa 28 ga watan Satumba 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.