Bayan Shafe Awa 24 a APC, Masoyin Pantami Ya Sake Komawa Gidan Malam

Bayan Shafe Awa 24 a APC, Masoyin Pantami Ya Sake Komawa Gidan Malam

  • Hon. Abubakar Sadiq Zakari ya koma tafiyar Pantamiyya da jam’iyyar PDP, bayan kwana daya sanar da ficewarsa
  • Zakari ya ce ya sake nazarin matsayar siyasarsa ne bayan tuntuba da shawarwari daga ’yan’uwa, abokai da manyan mutane
  • Ya nemi afuwar ’yan Pantamiyya da PDP, tare da jaddada cikakken goyon bayansa ga jagoransa, Farfesa Isa Ali Pantami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - Wani makusancin Farfesa Isa Ali Pantami ya koma gidan malam bayan sanar da ficewarsa daga tafiyar.

Hon. Abubakar Sadiq Zakari ya watsar da tafiyar gidan Malam inda ya yanke shawarar shiga jam'iyyar APC mai mulkin jihar.

Yaron Pantami ya koma PDP bayan barinta
Hon. Abubakar Zakari da Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Hon. Abubakar Sadiq Zakari.
Source: Facebook

Sai dai a wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, Hon. Zakari ya bayyana dalilansa na dawo wa gidan malam da tafiyar PDP.

Kara karanta wannan

Takarar Obi da Kwankwaso ta gamu da cikas, rikicin shugabanci ya raunana ta

Dalilin dawowar Zakari gidan Pantami

A cikin sanarwar, matashin ya ce ya yanke shawarar ce bayan yin nazari da kuma tattaunawa da yan uwa da abokan arziki.

Ya nemi afuwar yan Pantamiyya da magoya bayanta da kuma PDP inda ya ce yana jaddada goyon bayansa ga Farfesa Isa Ali Pantami.

Sanarwar ta ce:

"Bayan zama, tuntuba da shawarwari daga manyan mutane masu dattaku, ’yan uwa da abokan arziki dangane da matsayar siyasar da na ɗauka ta ficewa daga Pantamiyya da kuma jam’iyyar PDP, ina mai sanar da jama’a cewa na sake yin nazari kan matakin da na ɗauka.
"Saboda haka, ina neman afuwar dukkan ’yan Pantamiyya Movement da magoya bayanta, tare da sanar da cewa na dawo cikin tafiyar Pantamiyya Movement da jam’iyyar PDP.
Ina kuma jaddada cikakken goyon bayana ga jagorana, Farfesa Isa Ali Pantami, tare da ci gaba da girmama shi da kuma dukkan ’yan tafiyar."

Kara karanta wannan

Malami, mahaddaci kuma kwararre a karatun Kur'ani ya bar duniya a Gombe

Yaron Pantami ya dawo tafiyara bayan kwana 1 a APC
Dan takarar gwamnan PDP a Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Twitter

Afuwar da Zakari ya nema a siyasance

Hon Zakari ya kuma nemi afuwa bisa abin da ya faru kan lamarin, musamman ganin yadda lamarin ya jefa wasu daga cikin ’yan tafiyar da masoyanta cikin damuwa da jimami.

Ya ce ya samu kiraye-kiraye da shawarwari masu yawa daga ’yan’uwa, abokai da masoya, waɗanda suka nemi ya sake duba matsayar da ya ɗauka.

Matashin ya kuma yi wa mutanen jam'iyyar APC da na yi kwana daya a cikinsu fatan alheri bisa yadda suka tarbe shi inda ya bayyana godiya sosai da karimchi.

Ya kara da cewa:

"Ina mai tabbatar wa da kowa cewa wannan mataki na komawa cikin tafiyar an ɗauke shi ne cikin fahimta, mutunci da kuma kishin makomar siyasa ba don son rai ba."

Tsohon sanata ya dawo tafiyar Pantami

Mun ba ku labarin cewa tsohon Sanatan Gombe ta Arewa, Ambasada Haruna Garba, ya bayyana goyon bayansa ga Farfesa Isa Ali Pantami, tare da mika masa cikakken tsarin siyasar sa.

Kara karanta wannan

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya yi batan dabo, wata 2 ba a gan shi ba

Haruna Garba ya umarci magoya bayansa da su mara wa Pantami baya tare da hada kai da shi domin zaben 2027 da kuma bayan haka.

Sanatan ya ce ayyukan Pantami a mukaman da ya taba rike wa, da kuma kwarewarsa a harkokin cikin gida da na kasa da kasa, ne suka sa ya goyi bayansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.