Fayose Ya Fadi Yadda Tinubu Ya Bari APC Ta Fadi Zaben Osun
- Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce da Gwamnatin Tarayya tana da hanyoyin hana Accord lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka yi
- Ayodele Fayose ya bayyana cewa an buga sosai a zaben, wanda ke nufin cewa kowanne daga cikin yan takarar da ya tsaya wannan zabe zai iya nasara
- Tsohon gwamnan ya mika bukata da shawara ga Ademola Adeleke da ya samu nasarar lashe zaben wanda a ganinsa zai daukaka gwamnatinsa da Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun –Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce da Gwamnatin Tarayya na son yin amfani da karfinta wajen kwace zaben gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta, 2026, babu abin da zai iya hana ta yin hakan.
Sai dai Fayose ya ce zaben ya kasance mai matukar zafi inda aka fafara sosai, inda kuma hakan ta sa sakamakon zai iya karkata zuwa ga kowane bangare.

Source: Twitter
Jaridar daily Trust ta kawo labarin cewa tsohon gwamnan ya ce ya yi nazari kan zaben da ya ba Gwamna Ademola Adeleke damar lashe wa’adi na biyu.
Ayo Fayose ya magantu kan zaben Osun
Jaridar Punch ta wallafa cewa Fayose ya ce ya shafe lokaci a Osun kafin da lokacin zaben, inda ya rika zagayawa kasuwanni da al’ummomi domin jin ra’ayin jama’a kai tsaye, maimakon dogaro kawai da hasashen ‘yan siyasa.
Ya ce tattaunawarsa da mazauna jihar ta tabbatar masa da cewa zaben ya yi kusa sosai, har ba zai yiwu mutum ya yi hasashen wanda zai yi nasara kai tsaye ba.
Ya ce:
“Idan kana da zaben da yake 52 zuwa 48, kowane bangare na iya yin nasara."
Fayose ya shawarci gwamnan Osun
Fayose ya ce abin da ya fi karkatar da sakamakon zaben shi ne yadda kuri’u suka rabu a sassan jihar, musamman a Ede, wadda aka dade ana kallonta a matsayin jigo a siyasar iyalan Adeleke.

Kara karanta wannan
Kasar Birtaniya ta aiko saƙo Najeriya bayan APC ta sha kaye a zaben gwamnan jihar Osun
Ya ce tazarar kuri’un da Adeleke ya samu wajen lashe zaben ta kai kusan 66,000, inda kusan 46,000 daga cikin wannan tazara suka fito daga Ede.

Source: Instagram
A kalamansa:
“Duk wani hasashe zai nuna cewa ba abin mamaki ba ne idan aka samu irin wadannan alkaluma daga Ede."
Fayose ya kuma yi Allah wadai da tashe-tashen hankula da kashe-kashen da suka faru a lokacin zaben, yana mai bayyana su a matsayin abin takaici da ba dole ba.
Ya kuma taya Adeleke murnar nasarar, tare da bukatarsa da ya dauki nasarar a matsayin nauyin hada kan Osun, ba wai a matsayin nasara kan abokan hamayyarsa kawai ba.
Abin da Wike ya ce kan Osun
A wani labarin, kun ji cewa Nyesom Wike ya ce da Shugaba Bola Tinubu ya so APC ta lashe zaɓen Osun da ƙarfi, da ya taimaka masa, kuma Adeleke ba zai iya hana nasarar ba.
Wike ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta yi amfani da ƙarfinta wajen karkatar da zaɓen Osun ba, wanda Ademola Adeleke ya lashe duk da zafin siyasar da aka buga a neman zabe.
Ministan ya yi hasashen cewa zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da za a gudanar a watan Fabrairu, 2026 zai fi sauƙi ga Bola Ahmed Tinubu saboda ya ce jam’iyyun adawa sun raunana sosai.
Asali: Legit.ng
