Jirgin Sama Dauke da 'Yan Yawon Bude Ido Ya Rikito, Rayuka Sun Salwanta
- Jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari a Dutsen Ololokwe da ke Samburu a Kenya, inda dukkan mutane shida da ke cikinsa suka mutu
- Jami’an binciken hadurran jiragen sama sun ce har yanzu ba a tabbatar da sunayen wadanda suka mutu ba
- Rahotanni sun ce jirgin saman mai saukar ungulu na dauke da masu yawon bude ido ne a lokacin da ya yi hatsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Kenya - Wani jirgin helikwafta ya yi hatsari a Dutsen Ololokwe da ke gundumar Samburu a tsakiyar Kenya.
Jami'an kula da hadurran jiragen sama sun tabbatar da cewa Dukkanin mutane shida da ke cikinsa suka rasa rayukansu.
Sashen Binciken Hadurran Jiragen Sama na kasar ya ce har yanzu ba a tabbatar da sunayen mutanen da ke cikin jirgin ba, cewar rahoton tashar BBC.
Sai dai kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa masu yawon bude ido ne ke cikin helikwaftan.
Yadda hatsarin jirgin ya faru
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kenya (KCAA) ta ce hatsarin ya faru da misalin karfe 9:13 na safe agogon kasar, wato 6:13 na safe agogon GMT.
Ta ce jirgin na kan wani yawon shakatawa ta sama ne daga wani wurin kiwon namun daji a Losaiba zuwa Ewaso Nyiro, wani kogi da ke ratsa kusa da wasu wuraren ajiyar namun daji na kasa.
Wani hoton da aka wallafa a intanet ya nuna hayaki na tashi daga wurin da jirgin ya yi hatsarin a Dutsen Ololokwe.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta bayyana har yanzu ba a iya isa wurin da hatsarin ya faru ba, amma ana amfani da jirage marasa matuka wajen duba halin da wurin yake ciki.
KCAA ta ce jirgin da hatsarin ya rutsa da shi samfurin Eurocopter EC130 B4 ne, inda ta ce tana hada kai da hukumomin da abin ya shafa wajen gudanar da ayyukan ceto da bincike.
Ma’aikatar Sufuri da Sashen Binciken Hadurran Jiragen Sama ne za su jagoranci “bincike kan yanayin da ya jawo hatsarin”, in ji hukumar.
Dutsen Ololokwe ya shahara
Dutsen Ololokwe ya zama daya daga cikin wuraren da masu yawon bude ido suka fi ziyarta a Kenya a 'yan shekarun nan, musamman saboda irin yanayin shimfidar wurin da kuma kyawawan abubuwan da ake iya gani daga saman dutsen.
Ana kuma kiran dutsen da Ol Donyo Sabache. Dutse ne mai ban sha’awa mai saman da ya yi fadi, wanda ya yi fice a tsakiyar busasshiyar kasa ta gundumar Samburu.
Dutsen ya kuma zama sanannen wurin daukar hotuna da bidiyo, inda dubban masu ziyara ke zuwa domin daukar hoton yanayin da ya kebanta da wurin.
Hadurran helikwafta a Kenya
Hadurran jiragen helikwafta ba sabon abu ba ne a Kenya. A watan Fabrairu, wani helikwafta ya yi hatsari a gundumar Nandi da ke Rift Valley, inda mutane shida suka mutu, ciki har da wani dan majalisar dokokin kasar.
A shekarar 2024, shugaban rundunar sojin Kenya, Janar Francis Omondi Ogolla, ya mutu bayan wani helikwafta na soji da ke dauke da mutane 11 ya yi hatsari a yammacin kasar. Mutane biyu ne kawai suka tsira daga hatsarin.
A watan Yuni na shekarar 2021, akalla sojoji 10 suka mutu bayan wani helikwafta ya yi hatsari yayin da yake kokarin sauka a kusa da Nairobi, babban birnin kasar.
Asali: Legit.ng

