Tsohon Gwamna Ya Fadi Abin da Zai Hana Peter Obi Lashe Zaben Shugaban Kasa
- Ayodele Fayose ya ayyana Peter Obi a matsayin mutumin kwarai, amma ya ce ba shi da damar samun nasara a 2027
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa rabuwar kan 'yan hamayya a matsayin babban abin da zai kashe jam’iyyar NDC
- Fayose ya ce sai idan jam'iyyun hamayya sun hade waje guda za su iya kayar da APC mai mulki kuma yanzu sun makara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ayodele Peter Fayose wanda ya yi mulki sau biyu a Ekiti ya ce Peter Obi ya barar da damarsa ta cin zaben 2027.
Tsohon gwamnan na jihar Ekiti yana ganin yiwuwar nasarar Peter Obi ta ragu tunda ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar NDC daga ADC.

Source: Twitter
Ayo Fayose ya yi maganar zaben 2027
A yammacin ranar Talata Ayo Fayose ya yi wannan bayani da aka yi hira da shi a wani shirin na siyasa a gidan talabijin na TVC.

Kara karanta wannan
Duk da shan wahala a zaɓen Osun, Davido ya faɗi yadda Tinubu zai yi nasara a 2027
Da yake nazarin yadda zaben 2027 zai kasance, Fayose ya nuna kuskuren ‘yan adawar da suka fice daga cikin hadakar ADC.
‘Dan siyasar yake cewa da jagororin hamayyar sun yi zamansu a wuri guda, da sun fi samun damar kifar da Bola Tinubu a 2027.
Ya ce:
“Lokacin da dukkansu suke ADC, zan iya fada wa kowa cewa haduwarsu za ta yi dasiri.
Ranar da Obi ya bar jam’iyyar ADC zuwa NDC, a ranar ya sha kasa.”
Peter Obi ya sha yabon tsohon gwamnan Ekiti
Duk da haka, jaridar Punch da ta bibiyi hirar ta ce Fayose ya bayyana Obi a matsayin nagartaccen mutum da ya bar tarihi.
Tsohon jigon na PDP yake cewa ‘dan takaran na shugaban kasa a zaben 2023 ya nuna cewa za a iya gyara abubuwa a kasar.
Babban kalubalen da ya ce ‘yan adawa za su fuskanta shi ne kin hada-kai sun tunkari APC mai rike da mulki tun a 2015.

Source: Facebook
"Amma idan ‘yan adawa suka ki hada-kai, za su cigaba da shan kasa.
"Yanzu an makara sosai. INEC ta tantance kowa. Ko mutum ya ce ya janye, ya rage na shi.
"Dole a tsoma kafa a shiga ruwa. Ba za a iya fita ba. Tuni an riga an jike."
- Ayo Fayose
Ayo Fayose ya ba Bola Tinubu nasara
Da ake zancen takarar Bola Tinubu kuwa, Fayose ya yi wufe ya ce shugaban kasar zai zarce domin yana da goyon bayan jama’ansa.
Hasashen Mista Fayose ya ba Tinubu kuri’u miliyan hudu daga Kudu maso yamma da yake la’akari da abin da ya faru a zaben 2023.
'Dan Ganduje ya bar jam'iyyar NDC
Rahoton nan ya ce alakar ‘dan Abdullahi Ganduje da Rabiu Kwankwaso ta kare bayan kwanaki kimanin 80 kacal a jam’iyyar NDC.
A ranar Lahadin nan, Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje ya koma APC da ya yi murabus daga NDC a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Kara karanta wannan
Abin da ADC ta yi da ya taimaka wajen kayar da jam'iyyar APC a zaben gwamnan Osun
Shugabannin mazabarsa ta Gandje sun karbe shi kuma an ba shi katin zama 'dan jam'iyyar APC da mahaifinsa ya taba shugabanta.
Asali: Legit.ng
