Kotu Ta Tsare Tsohuwar Ƴar Takarar Gwamna a APC saboda Zarge Zarge

Kotu Ta Tsare Tsohuwar Ƴar Takarar Gwamna a APC saboda Zarge Zarge

  • Kotun Majistare da ke Ado-Ekiti ta tsare Abimbola Olajumoke, tsohuwar ’yar takarar gwamnan APC da aka cire, na tsawon wata guda
  • Ana zargin Olajumoke da bata suna, cin zarafin mutane ta yanar gizo da kuma hannu a satar mutane, bayan karar YSJ Agro-Allied Limited
  • Kotun ta dage sauraron karar zuwa 15 ga Satumba, yayin da kamfanin YSJ Farms ya ce yana neman dawo da gaskiya da kuma kare martabarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ekiti - Kotu ta tsare tsohuwar ’yar takarar gwamnan APC ta Ekiti kan zargin bata suna da cin zarafi a yanar gizo.

Kotun Majistare da ke Ado-Ekiti ta tsare Abimbola Olajumoke, tsohuwar ’yar takarar gwamnan APC a Ekiti, a gidan yari na tsawon wata guda.

An tsare tsohuwar yar takarar gwamnan APC a kotu
Taswirar jihar Ekiti da APC ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Tuhumar da ake yi wa Olajumoke a Ekiti

Kara karanta wannan

Ainihin dalilin gwamna Nasir Idris na sauya mataimakinsa a 2027

Ana tuhumar Olajumoke da bata suna, cin zarafin mutane ta yanar gizo da kuma satar mutane, sakamakon karar da Yemisi Joluwe ta shigar, cewar Channels TV.

Joluwe ita ce babbar jami’ar YSJ Agro-Allied Limited, kuma ita ce ta shigar da karar kan abin da ta bayyana a matsayin kalaman karya.

Alkalin Kotun Majistare, Abayin Adeosun, ya taba bayar da belin Olajumoke, amma daga baya ya soke belin bayan ta kasa bayyana a zaman kotun.

Bayan soke belin, jami’an tsaro sun kama Olajumoke ta jam'iyyar APC tare da tsare ta, yayin da kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa 15 ga Satumba.

Da take magana kan karar, Joluwe ta ce ta garzaya kotu ne domin neman adalci kan kalaman karya da ta ce sun bata mata suna.

Ta ce kalaman sun kuma shafi wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin, tana mai cewa YSJ Farms na maraba da suka mai ma’ana da binciken jama’a.

An tsare tsohuwar yar takarar gwamnan APC a Ekiti
Sufeta-janar na ƴan sandan Najeriya, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Olajumoke ta yi martani mai zafi

A cewarta, akwai bambanci tsakanin korafi na gaskiya da kuma yunkurin da gangan na lalata martabar kamfanin da aka kwashe shekaru ana ginawa.

Kara karanta wannan

APC ta saba da Tinubu kan zaben Osun, ta bayyana matsayarta kan nasarar Adeleke

Joluwe ta zargi Olajumoke da yin kalaman da suka kasance “karya tsantsa”, tare da cewa an yi hakan ne domin bata martabar kamfanin.

Ta ce kamfanin na da nauyin kare muradun masu zuba jari, ma’aikata da abokan cinikinsa daga zargin bata suna maras tushe.

Joluwe ta ce shari’ar ba ta kawo cikas ga ayyukan kamfanin ba, domin YSJ Farms na ci gaba da aikin noma da samar da abinci.

Ta kara da cewa kamfanin na kuma mayar da hankali wajen karfafa gwiwar matasa a Ekiti, tare da tabbatar wa abokan huldarsa da masu ruwa da tsaki da komai yana tafiya daidai.

Ta ce babban burinsu shi ne dawo da gaskiya gaba daya, tare da neman a janye zarge-zargen, a nemi afuwa a bainar jama’a sannan a biya diyya.

Dangane da zargin satar mutane da kuma kisan wani ma’aikacin gonar, Joluwe ta ce hukumomin tsaro na gudanar da bincike kan lamarin, cewar Punch.

An kai dan majalisa kotu bayan barin APC

An ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan karar PDP da ke neman a kwace kujerar ɗan majalisar Benue, Anthony Attah, bayan ya koma APC.

Kara karanta wannan

Abin kunya: An kama matashin da ya shiga gida satar ɗan kamfan matar aure

Kotun ta ce kundin tsarin mulki ya bai wa kakakin majalisar Benue da majalisar ikon ayyana kujerar babu kowa, ba kotu ba.

Alkalin ya ce INEC ba za ta iya shirya zaben cike gurbi ba sai bayan majalisar ta ayyana kujerar babu kowa sannan kakaki ya sanar da hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.