‘Yan Sanda Sun Fadi Hakikanin Dalilin Kama Masu Sanye da Rigar #TinubuMustGo

‘Yan Sanda Sun Fadi Hakikanin Dalilin Kama Masu Sanye da Rigar #TinubuMustGo

  • ‘Yan sandan Najeriya sun yi karin bayani game da kama mutane masu rigar #TinubuMustGo da aka yi a Borno
  • Jami’an tsaron sun ce aikinsu bai da alaka da siyasa, ana zargin matasa da aikata laifuffuka kuma an kai kotu
  • ASP Nahum Kenneth Daso ya ce ana zargin wadanda aka kama da mallakar kwayoyi da kuma neman kawo hargitsi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Borno - Rundunar ’yan sanda ta reshen jihar Borno ta kare kama wasu matasa biyar da suka sanya rigar #TinubuMustGo.

Jami’an tsaron sun bayyana cewa matakin da suka dauka ba shi da alaƙa da ra’ayinsu na siyasa kamar yadda ake rayawa.

TinubuMustGo
Kwamishinan ‘yan sandan Borno da hoton rigar #TinubuMustGo Hoto: Abba Hikima/Tinubu Must Go
Source: Facebook

An samu 'yan 'TinubuMustGo da kwayoyi

’Yan sandan sun ce an kama mutanen ne bisa zargin mallakar miyagun ƙwayoyi kamar yadda jaridar Daily Trust ta fada.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kashe wani shugaban jam'iyyar su Kwankwaso a Arewacin Najeriya

Baya ga samun da ƙwayoyi, an ce kuma sun aikata wasu laifuffuka da suka haɗa da tada tarzoma da hargitsa zaman lafiya.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ne ya bayyana hakan ranar Laraba.

A cewar rundunar, an kama mutanen biyar a ranar 25 ga Satumba 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma a wani samame.

Ya ce an kama mutanen ne bayan sun aikata abubuwan da ake ganin za su iya jawo tashin hankali da karya zaman lafiya.

'Yan sanda sun ce sun ga wiwi da kwayoyi

’Yan sandan sun ce sun kwato abubuwa da dama daga hannunsu. Daga cikinsu akwai kunshin ganyen da ake zargin tabar wiwi ne.

Haka kuma akwai ƙwayoyi 100 da ake zargin D5 ne da tukunyar shisha da almakashi. Wannan labari ya zo a jaridar nan ta Punch.

Kara karanta wannan

2027: Rarara ya sake fitowa da maganganu masu zafi kan 'yan Arewa da Tinubu

Haka kuma, ’yan sandan na jihar Borno sun ce sun kwato riguna na T-shirt guda biyu da ke ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go”.

Jami'an 'yan sanda sun damka wa alkali lamarin

Rundunar ta ce bayan gudanar da bincike na farko da karɓar bayanan waɗanda ake zargin, an gurfanar da su a gaban kotu.

’Yan sandan sun ce an gurfanar da mutanen bisa zargin haɗa baki wajen aikata laifi, tayar da tarzoma, daba da hana zaman lafiya.

Sai dai lauyoyin mutanen sun shigar da bukatar a ba su beli. Alƙalin ya ɗage sauraron batun belin zuwa ranar 6 ga Oktoba 2026.

Rundunar ’yan sandan ta ce ba ta nuna wariya ga kowa saboda ra’ayinsa na siyasa. Ta kuma ce tana mutunta ’yancin ɗan Adam.

Ta bukaci jama’a da su riƙa dogaro da sahihan bayanai maimakon jita-jita, tana cewa kotu ce za ta yanke hukunci busa hujjoji.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun kashe wani matashi mai shayi a jihar Adamawa

ADC ta yi tir da cafke masu

An ji cewa reshen jam’iyyar ADC ta Jihar Borno ta yi Allah-wadai da kama matasa biyar a Maiduguri saboda sanya rigunan "Tinubu Must Go".

ADC ta bayyana cewa kama matasan ya saba wa sashi na 39(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya ba ’yan ƙasa ’yancin faɗin ra’ayinsu.

Jam’iyyar ta bukaci jami’an tsaro da su saki matasan cikin hanzari ba tare da wani sharadi ba. Zuwa yanzu dai wannan bai samu karbuwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng