Muhammad Malumfashi
19969 articles published since 15 Yun 2016
19969 articles published since 15 Yun 2016
Labari ya zo daga Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano cewa Jami’an tsaro sun damke wasu mutane da ake zargin sun fito yin zanga-zanga saboda hukuncin zaben gwamna.
Daga Junairu zuwa Satumban 2023, gwamnonin jihohi sun yi bindiga da abin da ya kusa kai Naira tiriliyan 2. Ana facaka da sunan abinci da hawa jirgi a shekarar nan.
A yanzu wasu magoya bayan NNPP suna murnar kotun daukaka kara ta ba su gaskiya wajen rubuta hukuncin shari’ar Kano, amma lauyoyi sun ce ba haka abin yake ba.
NNPP ta fusata, inda shi kuma Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara yayin da aka fara zanga-zanga a Kano saboda hukuncin da kotun daukaka kara ta zartar a ranar Juma'a.
Wuta ta lakume ofisoshi da kayan aiki da gobara ta tashi a Hukumar shari’ar Kano. Tashin gobarar a ranar Talata ya tsayar da ayyukan Hukumar cak.
NNPP, APC sun sha bam-bam kan matsayin Abba da Gawuna da takardun kotu suka fito. Haruna Dederi ya yi ikirarin Abba yana nan a kujerar Gwamnan Kano.
Nyesom Wike ya fadi biliyoyin da ake bukata a karasa gidan mataimakin shugaban kasa. Bayan shekaru 13 da bada kwangilar, har yau ba a karasa gidan a Abuja ba.
Yanzu babu abin da Bola Tinubu yake so kamar a ce an sa sunansa a cikin littafin nan na Guinness. Tinubu yana so ya bi sahun Hilda Baci da Hadimin magajinsa.
Za a ji yadda takardun hukuncin kotu su ka birkita magoya baya tsakanin APC da NNPP a Kano. Takardun da aka fitar sun nuna Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu gaskiya.
Muhammad Malumfashi
Samu kari