Amurka Ta Koma Tekun Asiya, Ta Kwace Manyan Jiragen Ruwan Iran Makare da Mai

Amurka Ta Koma Tekun Asiya, Ta Kwace Manyan Jiragen Ruwan Iran Makare da Mai

  • Rundunar sojin Amurka ta kama wasu manyan jiragen dakon man fetur na Iran guda uku a tekun Asiya, kusa da kasashen Indiya da Malesiya
  • Wadannan jiragen sun hada da Deep Sea, Sevin, da kuma Dorena wanda ke dauke da gangar mai har miliyan biyu, lamarin da zai girgiza Iran
  • Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ita ma kasar Iran ta sanar da cewa ta kame wasu jiragen ruwa guda biyu a mashigar Hormuz

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Asiya – Rundunar sojin Amurka ta tsananta takunkumin da ta sanya wa kasar Iran ta hanyar kame tare da sauya wa aƙalla manyan jiragen dakon man kasar guda uku hanya a tekun Asiya.

Wannan mataki, wanda majiyoyin tsaro da na sufurin teku suka tabbatar a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026, na nufin hana Iran fitar da danyen mai zuwa kasashen waje.

Kara karanta wannan

Janar Ahmad Vahidi: Kwamadan Iran mai zafi da ya hana Trump sakat

Amurka ta kwace wasu manyan jiragen ruwan Iran da ke makare da danyen mai.
Sojojin Amurka na rangadin tekun Arabia kusa da M/V Touska bayan sun kai hari kan jirgin Iran. Hoto: U.S. Navy via Getty Images
Source: Getty Images

Amurka ta kwace wasu jiragen Iran

Jiragen da lamarin ya shafa sun hada da katon jirgin nan mai suna Deep Sea, wanda aka gani a gabar tekun Malesiya mako guda da ya gabata, da kuma jirgin Sevin mai daukar gangar mai kusan miliyan daya, in ji rahoton Reuters.

Haka kuma, rundunar sojin Amurka ta tabbatar da cewa tana tsare da jirgin Dorena, wanda ke makare da gangar mai miliyan biyu, inda wani jirgin yakin Amurka yake yi masa rakiya a tekun Indiya bayan ya yi kokarin karya takunkumin.

Tun bayan ballewar yaki tsakanin Amurka da Isra'ila a bangare guda, da kuma Iran a daya bangaren kimanin watanni biyu da suka gabata, harkar sufurin man fetur ta duniya ta shiga cikin babban hadari.

Amurka ta kori jirage 29

Rufe mashigar tekun Hormuz ya dakatar da kashi daya cikin biyar na man fetur da iskar gas din da duniya ke amfani da su, wanda hakan ya haddasa tsadar rayuwa a fadin duniya.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: An samu baraka, Trump ya sauke shugaban sojin ruwan Amurka

Rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta walafa a shafinta na X cewa, tun fara sanya takunkumin tekun, dakarunta sun tilasta wa jiragen ruwa guda 29 juyawa ko komawa tashoshin da suka fito domin tabbatar da cewa babu wani kaya da ya shiga ko fita daga Iran.

Amurka ta dage wajen tabbatar da cewa jiragen Iran ba su bar Hormuz ba
Wani jirgin dakon mai a mashigar ruwan Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta mayar da martani

A nata bangaren, kasar Iran ta sanar a yau Laraba cewa ta kama wasu jiragen ruwa guda biyu da suka yi kokarin fita daga mashigar Hormuz, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Wannan shi ne karon farko da Iran ta fara kame jiragen ruwa tun bayan fara yakin, matakin da ta ce ta dauka ne a matsayin martani ga kame jirajenta da Amurka ke yi.

Masu lura da al'amura na ganin cewa wannan dambarwa tsakanin Amurka da Iran a teku na iya kara dagula shirye-shiryen tattaunawar zaman lafiya da ake sa ran yi a kasar Pakistan.

Iran ta bude wa jirgin ruwa wuta

A wani labari, mun ruwaito cewa, Iran ta harba harsasai kan wani jirgin dakon mai a yau Laraba, lamarin da ya ƙara dagula shirye-shiryen tattaunawar sulhu.

Wannan hari ya zo ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya tsawaita wa'adin tsagaita wuta domin bai wa Iran damar gabatar da shawarwarin zaman lafiya.

Mashigar tekun ta Hormuz, wadda kashi 20 na man fetur ɗin duniya ke bi ta cikinta, na ci gaba da kasancewa filin daga tun a ranar 28 ga Fabrairu 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com