An Soki Yadda Mata Suka 'Yi Rashin Kunya' Suka Fito da Dan Kamfai a Taron APC a Kano
- Ana cigaba da caccakar yadda wasu mata suka fito kan titi dauke da dan kamfai wajen taron jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano
- Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi tir da matakin da matan suka dauka, har ya ce hakan fada ne da addini
- Ya nuna cewa suna Allah wadai da duk wadanda suka dauki nauyin matan da abin da suka yi, yana rokon Allah ya kawo mafita ga jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Fitan mata da dan kamfai wajen taron jam'iyyar APC a Kano ya jawo kakkausar suka daga 'yan Arewacin Najeriya.
Malamai da masana sun fara magana tare da kira ga Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta daukar mataki kan abin da matan suka yi.

Kara karanta wannan
Alƙawarin da Garo ya yi wa Abba da 'yan Kano bayan zabo shi ya zama mataimakin gwamna

Source: Facebook
Shafin Arewa Source ya wallafa bidiyon tsokacin da Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi game da yadda matan suka rika bayyana dan kamfai a kan tititi a X.
Sukar fitar mata da dan kamfai
Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya bayyana cewa fita da dan kamfai da mata suka yi yada barna ne da badala, abin da ba a taba ganin irinsa ba a Kano.
Ya ce hakan zubar da mutuncin mace ne da addinin Musulunci:
"A yau wasu 'yan siyasa sun sa mata a sun fito bisa titi a jihar Kano suna daga dan kamfai.., tana nuna wa duniya tana rawa, wannan ba siyasa ba ne, fada ne da Musulunci,'
Malamin ya bayyana cewa kunya tana daga cikin laduban addinin Musulunci amma saboda jahilci da tambadewa, Arewacin mata sun fito suna daga dan kamfai.
Kiran malamin ga Abba Kabir Yusuf
Malamin ya bayyana cewa suna kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki mataki a kan abubuwan da matan suka yi a jihar Kano.
Yayin kira ga Abba Kabir ya dauki mataki, malamin ya ce:
"Muna kira zuwa gare shi da ya tsawata dangane da kazantar siyasa."

Source: Facebook
An tir da fitan mata da dan kamfai
Wani dan jihar Kano da ke karantarwa a jami'a a kasar Jamus, Dr Muhsin Ibrahim ya yi tir da abin da ya faru, yana kira da a dauki mataki.
Ya wallafa a Facebook cewa:
"Idan an yi ba daidai ba, ko ka yarda ka yi Allah wadai da abin ko ka yi shiru. Shi ya fi dacewa. Kada ka kare wannan abin, musamman kawai don wasu sun yi makamancinsa a baya.
"Rashin kunya dai matan can sun yi. Duk gidan Musulmin Bahaushe/Bafulatani ba a ganin ɗan kamfe ko rigar nono a fili. Allah ya ba su hikimar amfani da shi a ɓoye. Haka abin yake.
"Duk da siyasar Kano ta zama wani abu, wannan ɗaga dan kamfai da tiƙa-tiƙan mata suka yi, suna rawa suna waƙa, abin takaici ne.
"Dama Manzon Allah (SAW) ya ce: "idan ba ka da kunya, ka yi duk abin da kake so". To, ga shi nan kuwa mun gani. Tir!"
Ga gargadin da malamin ya yi a bidiyo:
An zabi Mataimakin gwamna a Kano
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwaman Kano, Abba Kabir Yusuf ya zabi sabon mataimakin gwamna bayan murabus din Aminu Gwarzo.
Murtala Sule Garo da ake kira da kwamanda da ya rike mukamai da dama a baya ne ya zama sabon mataimakin Abba Kabir Yusuf.
An samu sauyin mataimakin gwamna a jihar Kano ne bayan Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC, dalilin da ya jawo wa Hon. Gwarzo yin murabus.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

