Hujjojin da Aka Samu a Takardun CTC Sun Nuna ba a Tsige Abba ba Inji Gwamnatin Kano

Hujjojin da Aka Samu a Takardun CTC Sun Nuna ba a Tsige Abba ba Inji Gwamnatin Kano

  • Wasu ‘yan NNPP sun yi ikirarin Abba Kabir Yusuf yana nan a kujerar Gwamna bayan hukuncin kotun daukaka kara
  • Kwamishinan shari’a ya ce APC ba ta tsige Gwamnan jihar Kano ba kamar yadda bayanai su ka nuna a takardun CTC
  • Amma jiga-jigan APC sun ce an yi waje da Abba Kabir Yusuf, kuma za a gyara kuskuren da kotun daukaka kara ta yi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Takardun hukuncin kotu watau CTC da kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta fitar, ya jawo sabani tsakanin mutanen jihar Kano.

An ji yadda bayanan da aka samu a rubuce su ka haddasa rudani tsakanin magoya bayan NNPP da APC game da shari’ar zaben gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

‘Kuskuren’ da aka samu a takardun CTC ba ya nufin NNPP ta yi nasara a kotu, Lauya

Gwamnatin Kano
AG ya ce APC ba ta tsige Gwamnan Kano ba Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Hukuncin kotu: Matsayar Gwamnan Kano

Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnati, Haruna Isa-Dederi ya bayyana matsayarsu a sa’ilin da ya zanta da manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Nigerian ta ce Haruna Isa-Dederi ya shaidawa ‘yan jarida cewa bayanan da ke takardun CTC sun tabbatar da gaskiyarsu ne a kotu.

A cewar lauyan, kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da alkalan kotun sauraron korafin zabe su ka zartar a Kano kwanaki.

An rahoto Dederi ya na cewa an ruguza hukuncin karamar kotu kamar yadda NNPP ta bukata, kotu ta tabbatar da nasarar Abba Yusuf a zabe.

“Hujjojin da ke shafi na 67 na takardar shari’ar kotun daukaka kara da magatakarda, Jameel Ibrahim Umar ya sa wa hannu, ya tabbatar da nasarar Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin zababben gwamnan Kano.”

-Haruna Isa-Dederi

Kara karanta wannan

Takardun Kotu sun haddasa rudani tsakanin APC da NNPP a shari’ar Gwamnan Kano

APC da NNPP za a hadu a kotun koli

Kwamishinan ya ce shafi na 67 na hukuncin ya nuna babu maganar tunbuke gwamna.

A cewar Dederi, wannan zai taimakawa jam’iyyarsa ta NNPP wajen tabbatar da matsayinsu a kotu cewa ba APC ta lashe zaben Kano ba.

Abba: 'Gawuna ya yi nasara' - APC

Amma wani jigon APC ya shaidawa Daily Trust cewa Nasiru Gawuna ya yi galaba a kotu, illa iyaka an samu tuntuben alkalami ne a takardun.

‘Dan siyasar ya ce kotu ta amsa kuskurenta, kuma a ranar Laraba za a gabatar masu da ainihin takardun da ke kunshe da gyaran da aka yi.

...Alaka ta da Rabiu Kwankwaso ne - Abba

Ana da labari Abba Kabir Yusuf ya na ganin saboda biyayyarsa ga Rabiu Musa Kwankwaso ake son raba shi da kujerarsa ta hanyar kotu.

Abba Kabir Yusuf yake cewa dole su godewa Rabiu Kwankwaso, kuma dole su fada masa, su na alfahari da shi duk da barazanar da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel