Wike: N15bn Ake Bukata a Karasa Gidan Mataimakin Shugaban kasa da Aka Fara a 2013

Wike: N15bn Ake Bukata a Karasa Gidan Mataimakin Shugaban kasa da Aka Fara a 2013

  • An dade da bada kwangilar gina gidan mataimakin shugaban kasa a birnin Abuja, amma har yau ba a iya kammalawa ba
  • Nyesom Wike ya sha alwashin ganin an kawo karshen aikin, ya ce za su fitar da kudin kwangilar domin kamfanin ya gama
  • Tun bayan nada tsohon Gwamnan jihar Ribas watau Wike a matsayin Minista, ake ta ganin sauyi a babban birnin na Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Aikin ginin gidan mataimakin shugaban kasa da ake yi a birnin Abuja zai ci kusan N15bn kamar yadda Nyesom Wike ya bayyana.

Ministan harkokin birnin Abuja, Nyesom Wike ya bayyana haka da ya je duba aikin da aka fara tun 2010, This Day ta fitar da rahoton.

Kara karanta wannan

Bayan zama Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya fadi burin da ya rage masa a Duniya

Nyesom Wike
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike Hoto: @Topboychriss
Asali: Twitter

Shekara 13 ana gina gidan mataimakin shugaban kasa

Shekaru 13 da su ka wuce aka ba kamfanin Messrs Julius Berger wannan kwangila a Abuja, har zuwa yau dai ba a iya karasa aikin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Na zo ne domin ganin aikin, kuma mun fadawa ‘dan kwangilar za mu ba su kudi da kyau zuwa karshen watan nan saboda su kammala.
Abin da mu ke yi yanzu shi ne mun gabatar da kwarya-kwaryan kasafin kudi, kuma shugaban kasa ya amince ya aikawa majalisa.
Abin da mu ke roko shi ne a kyale mu kashe N61bn kafin karshen shekarar 2024, saboda mu na da kudin, za mu yi wasu ayyuka da su.
Saboda haka zuwa ranar 29 ga watan Mayu, an kammala wadannan ayyuka."

- Nyesom Wike

Nyesom Wike zai yi ayyuka a Abuja

NAN ta rahoto Nyesom Wike ya na cewa birnin tarayya ta na da fiye da N70bn a cikin N100bn na asusun Sukuk da ba a taba ba tukuna.

Kara karanta wannan

"Abin duniya ke rudar 'yan Najeriya", Buhari ya yi magana mai jan hankali kan zabukan shugaban kasa

Da zarar an fitar da wadannan kudi, Ministan ya ce za a ayi amfani da su wajen tituna, gadoji, wuraren shakatawa da wuraren bude ido.

Ministan birnin ya tabo batutuwa tun daga albashin ma’aikata zuwa daukar manyan lauyoyi da zai rika yi domin kare birnin Abuja a kotu.

Wike ya ba masallaci gudumuwa

Kwanakin baya sai ga rahoto cewa Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya yi abin a yaba da ba da gudunmawa ga masallaci a Abuja.

Wike ya kuma amince da makudan kudade don gyara cibiyar Kiristoci a Abuja, a cewarsa hakan zai taimaka wajen gyara wuraren addinan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel