Muhammad Malumfashi
19957 articles published since 15 Yun 2016
19957 articles published since 15 Yun 2016
Mun kawo gajeren tarihin Ahmed Usman Ododo da ya ci zaben gwamnan jihar Kogi. Ododo ya fito daga karamar hukumar Okene ne, saboda haka ya na cikin kabilar Ebira.
Babu maganar yajin-aikin kungiyar ASUU a jami’o’i Idan Bola Ahmed Tinubu ya na mulki. Tinubu ya je taron yaye daliban jami’ar FUTO, ya dauki alkawarin gyara ilmi.
Za a ji yadda ‘Yan siyasa ke ta sintiri a Aso Rock domin zama Jakadu zuwa kasashen waje. An ba Bola Tinubu shawarar wadanda ya kamata su zama Jakadun Najeriya.
Ana fama da barayi da ‘Yan bindiga a Najeriya, a haka ne wasu Sojoji sun dauke ‘dan jaridan fadar Shugaban kasa, sun yi masa fashi a Abuja a makon da ya wuce.
A safiyar yau ne kotun daukaka kara za ta yanke hukuncin zaben Kano, A baya an ji NNPP ta zargi Abdullahi Umar Ganduje da Abdullahi Abbas da shirin hargitsa Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta fitar da jawabi a jiya inda aka ji Abba Kabir Yusuf ya na so jama’a su zauna lafiya duk yadda zaman kotun daukaka kara ya kasance.
Mun jero korafin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mikawa kotu a kan zaben Kano, su ne hujjojin da Abba Kabir Yusuf zai so a duba wajen ruguza nasarar Nasiru Gawuna.
NNPP ta ce shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, sun umarci a kawo ‘yan daba saboda shari'ar zaben Kano.
A yau ne kotun daukaka kara za ta yi hukunci a kan zaben Gwamna na jihar Kano. Rabiu Kwankwaso ya dawo Najeriya daga kasar waje ana gobe shari’ar Abba v Gawuna
Muhammad Malumfashi
Samu kari