Gobara Ta Yi Barna Yayin da Wuta ta Ci Hukumar Shari’a a Jihar Kano

Gobara Ta Yi Barna Yayin da Wuta ta Ci Hukumar Shari’a a Jihar Kano

  • Wani bangare na hukumar shari’ar jihar Kano ya kama da wuta lokacin da jami’ai su ke bakin aiki a ranar Talata
  • Ana zargin wutan ya jawo asarar dukiyoyi masu yawa, kayan aiki tun daga tebura zuwa takardu duk sun salwanta
  • Ba a san abin da ya jawo barkewar gobarar ba, amma bayanai sun nuna an tura mota da ta yi kokarin kashe wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano – Labari ya zo cewa gobara ta kama hukumar shari’a ta jihar Kano, a sanadiyyar haka wani sashe ya kone kurmus.

Jaridar Aminiya ta ce daukacin ofisoshin da ake da su a yankin da wutar ta tashi, sun kone kurmus a sanadiyyar wannan hadari.

Kano.
Gobara a Kano Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Har zuwa safiyar Laraba da ake tattara rahoton, ba a san abin da ya jawo tashin wutan ba, ana tunanin hakan ya tsaida ayyuka.

Kara karanta wannan

‘Kuskuren’ da aka samu a takardun CTC ba ya nufin NNPP ta yi nasara a kotu, Lauya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin inda hukumar ta ke ya fadawa manema labarai cewa ana zaune kurum sai aka hango wuta ta na kamawa a jiya.

Abin ya faru ne a lokacin da jami'an tsaro ke kokarin kare rayuka da dukiya a Kano.

Jami'an Kano sun kashe gobarar

Majiyar ta fadawa jaridar cewa ba ayi wata-wata bai sai jami’an kwana-kwana a Kano su ka isa wurin domin a kashe gobarar.

“Mun idar da sallah ke nan sai muka hango hayaki na tashi daga cikin Hukumar.
“Kafin mu san abin yi har motar Hukumar Kashe Gobara ta shigo harabar hukumar inda suka shiga aiki.”

- Wani mazauni

Kano - Gobarar ta yi barna Inji DG

Mukaddashiyar Darakta-Janar ta hukumar, Batulu Isah Waziri, ta ce wutar ta kama ci ne a lokacin ta na tsakiyar aiki cikin ofishinta.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa wani hukuncin kisa kan kashe jami’an DSS 7 a shekarar 2015

Batulu Isah Waziri ta ke cewa a sanadiyyar gobarar, ofisoshin wasu darektoci biyu na hukumar sun kone tare da kayan da su ke ciki.

Kayan aiki kamar tebur, kujeru da takardu dun sun kone kurmus da wutar ta tashi.

Bayanai za su fito daga baya

Saminu Yusuf Abdullahi wanda shi ne mai magana da yawun bakin hukumar da ke da alhakin kashe gobara ya tabbatar da lamarin.

Malam Saminu Abdullahi ya ce da zarar sun gama bincike, za su sanar da 'yan jarida irin asarar dukiya da makamantansu da aka yi.

Rudani kan shari'a a jihar Kano

Dazu nan aka ji labari takardun CCT sun ce kotun daukaka ta rushe Hukuncin kotun karafin zabe a kan tsige Gwamnan jihar Kano

Bayanan da aka samu daga kotu a rubuce sun ce an karbi hujjojin Abba Kabir Yusuf, APC za ta biya shi N1m, akasin hukuncin da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel