Gwamnoni Sun Kashe Naira Tirilyan 1.7 a Wajen Cin Abinci da Tafiye-Tafiye a Watanni 9

Gwamnoni Sun Kashe Naira Tirilyan 1.7 a Wajen Cin Abinci da Tafiye-Tafiye a Watanni 9

  • Daga Junairu zuwa Satumban 2023, gwamnonin jihohi sun yi bindiga da abin da ya kusa kai Naira tiriliyan 2
  • Abubuwan da ke cin kudin gwamnatoci sun hada da biyan albashi da alawus, idan aka hada an kashe N800bn
  • Kudin sayen katin waya, intanet, cin abinci, tafiye-tafiye, jiragen sama suna cikin abubuwan da ke cin kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jihohi 36 da ake da su a Najeriya sun batar da N1.71tr a kan alawus, tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare a shekarar nan ta 2023.

Wani dogon rahoto da mu ka samu daga Punch ya nuna gwamnonin jihohin sun kashe kudi a sayen kayan aiki da gyaran jiragen sama.

Tinubu
Tinubu da wasu Gwamnoni Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Gwamnoni sun kashe N2tr a watanni

Kara karanta wannan

Wani bafullatani ya datse hannun abokinsa kan lemun kwalba a jihar Ogun

Gwamnatocin sun kashe wadannan makudan kudi ne daga Junairu zuwa Satumban bana yayin da gwamnati ke kukan karancin kudi a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu wadannan bayanai ne daga shafin budgIT, wadanda su ke bin diddikin kudin da gwamnatocin jihohi da na tarayya su ke kashewa.

Jaridar ta yi nazari na musamman a kan jihohi 24 domin gano yadda ake facaka da kudi.

Albashi ya cinye N800bn a jihohi

A tsawon wannan lokaci na watanni tara, gwamnonin sun kashe N802.43bn a wajen biyan albashi, hakan na nufin jihohin sun kashe N2.52tr.

Wasu wuraren da gwamnoni ke kashe kudi sun hada da alawus iri-iri; sayen kaya, zuwa taro, sayen katin waya da kudin wuta da intanet.

Gwamnoni sun ci bashin kusan N1tr

Rahoton ya ce jihohi 30 sun raba kudin tsaro na N87.45bn sannan sun ci bashin N988bn. Masana suna ganin gwamnoni na facaka da dukiya.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa wani hukuncin kisa kan kashe jami’an DSS 7 a shekarar 2015

Abia ta kashe N17.61bn a biyan hayan gida, abinci, alawus, fansho, giratuti, kudin waya da hawa yanar gizo, tafiye-tafiye, fetur da sauransu.

A watanni shida, Akwa Ibom ta kashe N92.54bn da sunan alawus, zirga-zirga, kayan aikin ofis da asibitoci da N851m a kan siyasa da nishadi.

Kusan babu Gwamnan da aka bari a baya

Gwamnatocin Adamawa, Anambra, Borno, Benuwai, Enugu da Nasarawa sun kashe makudan kudi a albashi, bukukuwa da tafiye-tafiye.

Haka zalika ba a bar jihohi irinsu Kaduna, Kano da Katsina wajen kashe biliyoyin kudin ba.

Gwamnan Tinubu a Jihar Legas

A makon nan aka samu labari cewa Bola Tinubu zai so sunansa ya shiga cikin littafin tarihin Guinness saboda kokarin da ya yi a jihar Legas.

Tinubu ya ce ya yi abin a yaba wajen gyara Legas da ya na gwamna tsakanin 1999 da 2007, shugaban ya ce zai so ya cusa sunansa da kan shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel