Yadda Alkalin Alkakai Ya Dauko ‘Danuwansa Ya Yanke Hukunci a Shari’ar Zaben Kano

Yadda Alkalin Alkakai Ya Dauko ‘Danuwansa Ya Yanke Hukunci a Shari’ar Zaben Kano

  • Lateef Adebayo Ganiyu yana cikin Alkalan da su ka tsige Abba Kabir Yusuf a kotun daukaka kara da ke zama a Abuja
  • Chidi Odinakalu ya ce akwai alaka tsakanin Alkalin da kuma shugaban Alkalin Alkalai na kasa watau Kayode Ariwoola
  • Farfesa Odinakalu wanda ya soki shari’ar Gwamna Yusuf ya fito da hujjoji da za su tabbatar da abubuwan da yake fada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Chidi Odinakalu ya bayyana cewa daya daga cikin Alkalan da su ka saurari shari’ar zaben Kano yana da alaka da Alkalin Alkalai.

Farfesa Chidi Odinakalu ya ce Lateef Adebayo Ganiyu ‘da ne ga shugaban Alkalai na kasa, Kayode Ariwoola wanda ya shiga ofis a 2022.

Kara karanta wannan

Kuskuren Cikin Takardun Hukuncin Kano Ba Tuntuben Alkalami ba ne - Farfesa Odinkalu

Buhari ya nada CJN
Nada Alkalin Alkakai Hoto: Ali Tolani
Asali: Twitter

Alkalin zaben Kano 'danuwan CJN ne?

Masanin shari’ar yake fada a Twitter cewa Lateef Adebayo Ganiyu ya fito ne daga Iseyin a Oyo, garin da shugaban Alkalan kasar ya fito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, a Satumban shekarar nan aka nada Lateef Ganiyu ya zama Alkalai a kotun daukaka kara tare da wani surukin Alkalin Alkalan.

Wanene Lateef Adebayo Ganiyu?

Mai shari’an ya yi digiri a jami’ar Legas a 1992, a shekarar 1993 Ganiyu ya fara aiki. Daga baya ya yi digirgi a jami’ar Obafemi Awolowo a 1997.

A shekarar 2018 lokacin Marigayi Abiola Ajimobi ya na gwamna ya nada Lateef Ganiyu da wasu a matsayin alkalan babban kotun jihar Oyo.

Shi ne Alkalin da ya yi watsi da wata kara da aka kai Adebayo Shittu a kan rikicin fili, ya yi shekaru takwas kafin zuwansa kotun daukaka kara.

Kara karanta wannan

Mataimakin Sanusi a bankin CBN ya fito ya soki hukuncin zaben gwamnan jihar Kano

Shari'ar zaben Gwamnan Kano

Kwanaki kadan da rantsar da Alkalin, sai ga shi ya shiga cikin wadanda su ka saurari shari’ar Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar APC a Kano.

Bayanai sun tabbatar da ikirarin na Odinakalu domin kuwa Legit ta gano Alkalin ya yi aiki ne a manyan kotun jihar Oyo daga 2016 zuwa 2023.

Alkalin mai shekara 57 ya na cikin wadanda su ka tabbatar da hukuncin kotun zabe wajen tsige Abba Kabir Yusuf daga gwamnan jihar Kano.

Hukuncin ya jawo surutu daga masana shari’a da zanga-zanga wajen magoya bayan NNPP yayin da aka daukaka shari'a zuwa gaban kotun koli.

Hukuncin zaben Kano kuskuren alkalami ne?

Ana da labari Farfesan ya ce ba kuskure kotu ta yi a shari’ar zaben Kano ba, yana ganin da walakin wai goro a miya a shari’ar zaben na Kano.

Chidi Odinkalu ya ce kananan kura-kurai ake gyarawa na subutar alkalami ba manyan tafka da warwaran da ya jawo surutu a kasar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel