Lauyoyin NNPP Sun Daukaka Kara a Kotun Koli Kan Tsige Gwamna Abba

Lauyoyin NNPP Sun Daukaka Kara a Kotun Koli Kan Tsige Gwamna Abba

  • NNPP ta dauki matakin zuwa kotun koli a kan tsige Gwamnan Kano watau Abba Kabir Yusuf da aka yi a baya
  • Lauyoyin jam'iyyar sun shigar da kara kamar yadda bayanai su ka nuna bayan an samu tuntuben alkaluma a CTC
  • Idan masu kare Abba Yusuf sun yi nasara, za a wargaza hukuncin da kotunan baya su ka yi a kan zaben Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Lauyoyin jam’iyyar NNPP a shari’ar zaben gwamnan Kano sun garzaya kotun koli domin daukaka hukuncin da aka yi a baya.

Bayanan da aka samu daga shafin Ibrahim Adam, daya daga cikin na kusa da gwamnatin Kano da Rabiu Kwankwaso sun shaida haka.

Kara karanta wannan

Kano: Yayin da CTC ta tabbatar da nasarar Abba Kabir, NNPP ta fadi hanyar warware matsalar

Lauyoyin da ke kare jam’iyyar NNPP a karkashin jagorancin Wale Olanipekun SAN sun tafi kotun koli domin soke nasarar da aka ba APC.

Abba Kabir Yusuf
Kotu ta tsige NNPP da Gwamnan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Abba ya shigar da kara a kotun koli

Kotun daukaka kara da kotun zabe duk sun tsige Abba Kabir Yusuf, aka zartar da hukunci cewa Nasiru Gawuna ne halataccen gwamna.

A cikin wadanda ake kara a shari’ar akwai jam’iyyar APC mai mulkin kasa da hukumar INEC da ta ba NNPP nasara a zaben na Kano.

Takardun da aka gabatar sun nuna NNPP ta na da korafi goma a kan hukuncin da aka yi a ranar Juma’ar da ta wuce, 17 ga Nuwamba.

Abba 'dan jam'iyyar NNPP ne?

Lauyoyin na NNPP sun roki a rusa hukuncin, kuma ayi watsi da maganar kudin da aka bukaci wanda ya shigar da kara ya biya APC.

Kara karanta wannan

‘Kuskuren’ da aka samu a takardun CTC ba ya nufin NNPP ta yi nasara a kotu, Lauya

A korafin lauyoyi masu kara, kotun korafin zabe ba ta ba jam’iyyar APC gaskiya a kan batun zaman Abba Kabir Yusuf ‘dan NNPP mai-ci ba.

Wani korafi na NNPP shi ne wadanda ake tuhuma ba su bijiro da zargin ba, kuma alkalan kotun ba su da ikon sauraron batun rajistar jam’iyya.

Wani mataki NNPP ta dauka?

BBC Hausa ta ce jam’iyyar NNPP ta kira taron manema labarai, ta kuma nemi majalisar shari’a ta binciki hukuncin zaben gwamnan Kano.

A daidai lokacin da labarin nan yake zuwa mana, mun fahimci wasu mazauna sun fara zanga-zangar lumana a Kano a kan hukuncin kotun.

Magoya bayan NNPP sun zargi jami'an tsaro da watsa masu borkonon tsohuwa a titi.

Tafka da warwara kan shari'ar Kano

Ana da labari cewa takardun CCT sun ce kotun daukaka ta rushe Hukuncin kotun karafin zabe a kan tsige Gwamnan Kano da aka yi kwanaki.

Kara karanta wannan

Hujjojin da aka samu a takardun CTC sun nuna ba a tsige Abba ba – Gwamnatin Kano

Bayanan da aka samu daga kotu a rubuce sun ce an karbi hujjojin Abba Kabir Yusuf, APC za ta biya shi N1m, akasin hukuncin da aka yi a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel