Sanatoci Sun Gana da Tinubu, an Ruwaito Cewa Ya Yi Fatali da Bukatarsu kan Zaɓen 2027

Sanatoci Sun Gana da Tinubu, an Ruwaito Cewa Ya Yi Fatali da Bukatarsu kan Zaɓen 2027

  • Shugaba Bola Tinubu ya gana da Shugabannin majalisar dattawa a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya na Abuja
  • Wasu sanatocin sun nemi a ba su tikitin takara mai tsaye wanda aka ce shugaban bai amince ba kuma ya nace cewa dole a mutunta tsarin jam’iyya
  • Ganawar sirri da aka yi a Aso Villa ta mayar da hankali kan batutuwan kasa masu muhimmanci, inda aka ce an dauki matakai masu karfi ba tare da bayyana su ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya gana da shugabannin majalisar dattawa a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja, bayan zaman sirri da sanatoci suka gudanar a baya.

An bayyana ganawar a matsayin mai muhimmanci kuma ta gaggawa, inda aka ce ta biyo bayan wasu shawarwari da aka yanke a zaman sirri na majalisar.

Kara karanta wannan

Sanata Kalu ya sha rubdugu saboda yabon shugaba Tinubu

Tinubu ya gana da sanatoci a Abuja
Shugaba Bola Tinubu yayin da ganawa da shugabannin majalisar dattawa. Hoto: @aonanuga1956.
Source: Twitter

Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya tabbatar da faruwar ganawar a shafinsa na X amma bai bayyana cikakken bayani kan abin da aka tattauna ba.

Godswill Akpabio ya jagoranci ganawa da Bola Tinubu

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne ya jagoranci tawagar, wadda ta isa fadar shugaban kasa jim kadan bayan an dage zaman majalisar.

Sanata Opeyemi Bamidele ya ce an dauki matakai muhimmai a taron, yana mai cewa an tattauna batutuwa masu muhimmanci ga kasa.

Sauran sanatocin da suka halarci taron sun hada da Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu; Sanatan Kebbi ta Tsakiya, Adamu Aliero; Sanatan Gombe ta Tsakiya, Danjuma Goje; da kuma Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi.

Ana zargin Tinubu ya yi fatali da bukatar sanatoci a zabe
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da mataimakinsa, Barau Jibrin. Hoto: The Nigerian Senate.
Source: Facebook

Zargin da ake yi kan ganawar Tinubu, sanatoci

Sai dai wata majiya daga majalisar dokoki da Sahara Reportera ta samu ta bayyana cewa manufar ganawar ita ce neman tabbacin samun tikitin takara kai tsaye ga sanatoci.

Kara karanta wannan

2027: Kano da wasu jihohin Arewa 7 da majalisa ke son haramta wa yin kamfen

Majiyar ta ce sanatocin sun gabatar da hujjoji kan muhimmancin ci gaba da kwanciyar hankali, tare da neman a ba su damar tsayawa takara ba tare da hamayya ba.

Sai dai an ce Shugaba Tinubu ya yi watsi da bukatar, yana mai cewa gwamnonin jihohi su ne shugabannin jam’iyya a jihohinsu kuma dole su na da tasiri.

Ya kara da cewa gwamnoni su na da hakkin yanke hukunci kan wanda zai samu tikitin takara a karkashin tsarin jam’iyya wanda aka dade ana bi.

Batun tikitin kai tsaye ya dade yana jawo cece-kuce a siyasar Najeriya, inda wasu ke ganin yana rage dimokuradiyya, yayin da wasu ke kare shi.

APC ta musanta ba da tikiti kai tsaye

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC ta yi karin haske kan jita-jitar da ake yadawa game da tikitin takara ga wasu yan siyasa a kasar.

APC ta yi magana ne kan rahoton cewa za ta ba gwamnoni da ‘yan majalisa tikitin kai tsaye a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Mataimakin shugaban APC na kasa (Kudu), Ben Nwoye, ya ce tsarin tikitin kai tsaye ba ya cikin kundin tsarin jam’iyya ko doka, kuma dole a bi ka’ida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.