Kano: ‘Yan Sanda Sun Cafke Mutane Masu Zanga Zanga Saboda Kotu Ta Tsige Abba

Kano: ‘Yan Sanda Sun Cafke Mutane Masu Zanga Zanga Saboda Kotu Ta Tsige Abba

  • Jami’an tsaro sun damke wasu mutane da ake zargin sun fito yin zanga-zanga saboda hukuncin zaben gwamnan jihar Kano
  • Wasu mutane ba su ji dadin tsige Abba-Kabir Yusuf da kotu tayi, aka ce Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ne halataccen gwamna a Kano ba
  • ‘Yan sanda sun haramta duk wani nau’in taron zanga-zanga ko murna saboda hukuncin, Kwamishina ya ce sun kama mutane

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - ‘Yan sanda su yi nasarar cafke wasu mutane da aka samu suna zanga-zanga a kan hukuncin zaben gwamna na jihar Kano.

Rahoton Vanguard ya tabbatar da cewa mutane bakwai suna hannun jami’an ‘yan sanda saboda sun fita zanga-zanga a kan tituna.

Gwamnan Kano
Ana zanga-zanga saboda tsige Gwamnan Kano Hoto: @KYusufAbba
Asali: Facebook

Menene ya jawo zanga-zanga a Kano?

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana zanga-zanga a Kano kan tsige Abba Gida Gida, bidiyo ya bayyana

Masu zanga-zangar sun yi tir da yadda aka yanke shari’ar Abba-Kabir Yusuf da kuma Nasiru Yusuf Gawuna a kotun daukaka kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana da labari cewa ‘yan sanda sun watsawa wadannan mutane borkonon tsohuwa da ruwa domin su watse daga kan titunan jihar.

Hukumar dillacin labarai ta ce masu zanga-zangar sun bukaci a sake duba hukuncin alkalai a shari’ar zaben gwamnan Kano na 2023.

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya yi magana

Kwamishinan ‘yan sanda na reshen Kano, Hussaini Gumel ya shaidawa manema labarai ta wayar salula cewa sun cafke wasunsu.

CP Hussaini Gumel ya shaidawa NAN an yi ram da su ne yayin da su ka kama hanyar zuwa gidan gwamnatin Kano a ranar Larabar nan.

"Mun yi nasarar hana zanga-zangar, kuma mu na rike da mutum bakwai daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Lauyoyin NNPP Sun Daukaka Kara a Kotun Koli Kan Tsige Abba

Mun tura jami’ai da makamai zuwa yankin; kuma tuni mun fara bincike mai zurfi, za mu sanar da ku cigaban da aka samu nan gaba."

- CP Hussaini Gumel

Kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira ga mutane su cigaba da harkokin gabansu, ya ce an dauki matakan hana irin haka faruwa a Kano.

Gwamnan Kano ya tafi kotun koli

Tun a yammacin Laraba rahoto ya zo cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara yayin da aka fara zanga-zanga a kan tsige NNPP.

Jam'iyyar NNPP da lauyoyinta ba su gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ba, sun roki a tsige APC. Ana sa ran zuwa Disamba a yi hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel