Takardun Kotu Sun Haddasa Rudani Tsakanin APC da NNPP a Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

Takardun Kotu Sun Haddasa Rudani Tsakanin APC da NNPP a Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

  • Jameel Ibrahim Umar ya fitar da takardun CTC na hukuncin shari’ar zaben Gwamnan Kano a kotun daukaka kara da ke Abuja
  • Takardun da aka fitar sun nuna Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu gaskiya duk da cewa a kotu an yi watsi da korafin lauyoyinsa
  • Masana suna ganin tuntuben alkalami aka samu a takardun hukuncin, amma jam’iyyar NNPP ta fassara abin da yin nasara a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - An samu rudani a jihar Kano a dalilin takardun shari’a watau CTC da aka fitar da karar Abba Kabir Yusuf v Nasiru Yusuf Gawuna.

Rahoto daga Daily Trust ya nuna takardun da aka fitar sun nuna tafka da warwara da aka samu daga alkalan kotun daukaka kara a Abuja.

Kara karanta wannan

Kano: NNPP Ta Koka Kan Makarkashiyar da Aka Shirya Mata Kafin Shiga Kotun Koli

Abin da aka zartar a kotun daukaka karan shi ne an yi watsi da korafin Abba Kabir Yusuf, aka tabbatar da tsige shi daga kan karagar mulki.

Kano.
Kano: Nasiru Gawuna ya doke Abba Kabir Yusuf a kotu Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yi tafka da warwara a shari'ar Kano

A shafi na 68 na CTC, an rubuta cewa Mai shari’a Moore Aseimo Abraham Adumein ya ce an ba wanda ake kara watau APC gaskiya a karar.

Can gaba kadan kuma rahoton ya ce sai aka rubuta: “La’akari da haka, na ba mai kara gaskiya a kan wanda ake tuhuma (APC) a shari’ar.

Ba ayi nisa ba kuma sai alkali ya ce “saboda haka babu hujjoji a korafin nan, na yi watsi da daukaka karar”. Abin nufi, APC ta sake yin nasara.

“An yanke hukunci cewa na farko da aka yi kara zai biyya diyyar N1m ga wanda ya shigar da kara”. A nan ma an samu tafka da warwara a CTC.

Kara karanta wannan

Shari’ar Kano: Kuskuren da aka yi a kotu wajen tsige Gwamna Abba – Femi Falana

Idan da za a bi wannan bayani, jam’iyyar APC ce za ta biya Gwamna Abba Yusuf kudi, wanda a zahirin shari’ar da aka yi, akasin haka ya faru.

NNPP da Abba sun yi nasara a Kano?

Wanda yake kara shi ne Abba Kabir Yusuf, na farko a tuhumar kuwa ita ce jam’iyyar APC.

Solacebase ta ce Kwamishinan shari’a na Kano, Haruna Dederi ya ce takardun sun nuna an yi watsi da tsige Abba da kotun korafin zabe ta yi.

Amma APC ta ce tuntuben alkalami ne aka samu daga kotu wanda ake sa ran gyarawa.

APC v NNPP: Masani ya yi karin haske

Shamsuddeen Gambo Mairoba ya rubuta a shafin Facebook:

"A fahimtata wannan kuskure ne kotun daukaka kara tayi. Da wuya ka dauki hukuncin kotu ka karanta baka samu kuskure ba. Ba’a karanta zabar wani bangare na hukunci a karanta a manta da sauran. Duka sauran bangarorin wannan hukunci ya nuna AKY bai yi nasara a Appeal ba. Saboda haka, doka tayi tanaji na abun da ake kira Slip Rule wanda shine idan an samu kuskure ko tuntuben alkalami a hukunci, to ana iya gyara wannan kuskuren musamman idan ma’anar hukuncin ta bayyana.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan APC Ya Yi Allah Wadai da Kotu a Kan Tsige Gwamnonin PDP da NNPP

Saboda haka, gara a bawa ainihin daukaka wannan kara muhimmanci fiye da wannan."

Meyasa ake son tsige Gwamnan Kano?

A cewar Gwamnan Kano, saboda Rabiu Kwankwaso ake son raba shi da mulki ta hanyar shari’ar zabe, a farkon makon nan aka samu rahoton nan.

Fadar shugaban kasa ta karyata zargin da ake yi, ta ce dokar kasa ce ta ci NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng