Shari’ar Ministan Buhari Ta Zo da Mamaki, Kotu Ta Watsa wa EFCC Kasa a Ido
- Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da muhimman hujjojin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC
- Matakin ya biy bayan ci gaba da shari’ar zargin damfarar kwangila N2.8bn da ake yi wa Hadi Sirika da wasu mutane
- Kotun ta ce bayanan da aka karɓo daga ‘yar Sirika da mijinta ba su cika sharuddan doka ba, saboda rashin bin tanadin doka da yadda ake ɗaukar ibayanai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata babbar kotun Abuja da ke Maitama ta yi watsi da wasu muhimman hujjoji da hukumar EFCC ta gabatar mata kan tuhumar Sanata Hadi Sirika.
Hukumar ta yi watsi da hujjojin ne a shari’ar zargin damfarar kwangila N2.8bn da ake yi wa tsohon ministan sufurin jiragen sama,huk Hadi Sirika.

Source: Facebook
Hujjojin da kotu ta ki karba daga EFCC
Hujjojin da aka ƙi amincewa da su sun haɗa da bayanan da aka ce ‘yarsa Fatima Sirika da mijinta Jalal Hamma sun bayar a ofishin hukumar EFCC, cewar Premium Times.
Mai shari’a Sylvanus Oriji ya ce ba a bi tanadin sashe na 15(4) na dokar ACJA 2015 ba wajen karɓar waɗannan bayanai wanda hakan ya saba doka matuka.
Ya ce:
“A bayyane yake daga shaidar da shaidan ya bayar cewa ba a bi tanadin sashe na 15(4) na dokar ACJA ta 2015 ba lokacin da jami’an EFCC suka karɓi bayanan waɗanda ake tuhuma na biyu da na uku.”
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan waɗanda ake tuhuma sun ƙalubalanci cewa an tilasta musu yin bayanan ne ba da son rai ba a lokacin.

Source: Twitter
EFCC ta bayyana muhimmancin hujjojin
Hukumar EFCC ta ce bayanan na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zargin da ake yi wa Sirika da sauran waɗanda ake tuhuma.

Kara karanta wannan
Hankalin iyalan mutum 416 da Boko Haram ta sace ya tashi yayin da wa'adi ya kusa cika
Sai dai lauyoyin masu kare kansu sun dage cewa dole ne a nadi bidiyo lokacin karɓar irin waɗannan bayanai, wanda ba a yi ba a wannan hali.
Bayan wannan hukunci, lauyan ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma ya nemi kotu ta soke dukkan hujjojin da aka gabatar, cewar Peoples Gazette.
A ƙarshe, kotu ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Yunin 2026 domin ci gaba da sauraron sauran buƙatu da ke gaban ta.
Hukumar DSS ta gurfanar da El-Rufai a kotu
Tun da farko, mun ba ku rahoto cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Hukuma DSS na zargin El-Rufai da laifuffuka biyar da suka shafi katsalandan da leken asiri kan tattaunawar wayar tarho ta mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
Wannan takun-saƙa ya samo asali ne daga iƙirarin da El-Rufai ya yi a gidan talabijin cewa ya saurari umarnin da Ribadu ya bayar na a kama shi.
Asali: Legit.ng
