Zaben 2027: Tinubu Ya Sanya Labule da Gwamnonin APC a Abuja
- Bayan ganawa da sanatoci, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ganawar sirri da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa
- Taron ya samu halartar gwamnoni da dama ciki har da Hope Uzodimma, Inuwa Yahaya da Babagana Zulum
- Har yanzu ba a bayyana manufar taron ba, amma ana kyautata zaton yana da alaka da shirye-shiryen zabe mai zuwa bayan ganawar gaggawa da sanatoci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ganawa a bayan fage da gwamnonin da aka zaba karkashin jam’iyyar APC.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gudanar da taron ne a fadar gwamnati da ke Abuja. Taron yana gudana ba tare da jama’a ba.

Source: Twitter
An tsara taron da farko ne da karfe 4:00 na yamma a dakin majalisar ministoci, amma daga baya aka mayar da shi zuwa dakin taron ofishin shugaban kasa, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Sanatoci sun gana da Tinubu, an ruwaito cewa ya yi fatali da bukatarsu kan zaɓen 2027
Bola Tinubu ya gana da sanatoci a Abuja
Ganawar ta yau ta biyo bayan wata ganawa ta gaggawa da shugaban kasa ya yi da shugabannin majalisar dattawa a ofishinsa cikin sirri kwanan nan.
Duk da rashin cikakkun bayanai, an ji cewa taron bai rasa nasaba da sababbun matakan shirye-shiryen zabe da ake yi gabanin babban zaben kasa mai zuwa.
Gwamnonin da suka halarci taro da Tinubu
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Shugaban kungiyar gwamnoni, Hope Uzodimma na Imo, Inuwa Yahaya na Gombe, da Farfesa Babagana Zulum na Borno.
Sauran sun hada da Hyacinth Alia na Benue, Biodun Oyebanji na Ekiti, Peter Mbah na Enugu, da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara tare da wasu.
Wasu jihohi sun samu wakilci ne ta hannun mataimakan gwamnoninsu maimakon gwamnonin kansu saboda wasu dalilai na daban da suka hana su halarta kai tsaye.

Source: Facebook
Abin da Tinubu ya fada wa gwamnoni
Gwamnan Niger, Umar Bago, ya shaida wa manema labarai abin da suka tattauna da shugaban kasa a fadarsa, cewar Daily Post.
Ya ce shugaban kasa ya sake jaddada goyon bayansa ga amfani da zaben kai tsaye ko tsarin sulhu wajen zaben ‘yan takarar jam’iyya.
Bago ya bayyana cewa shugaban ya jaddada muhimmancin hadin kai a cikin jam’iyyar, yana kira ga mambobi su rungumi hanyoyin da za su karfafa dankon zumunci da tabbatar da daidaito a matakai daban-daban na jam’iyya.
Ya kara da cewa gwamnoni suna goyon bayan wannan matsaya, tare da cewa za a ci gaba da tuntuba tsakanin shugabannin jam’iyya domin cimma matsaya daya kan hanyar zaben fidda gwani.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara tattaunawa a cikin APC dangane da hanyoyin gudanar da harkokin cikin gida na jam’iyya da kuma shirye-shiryen tunkarar zabukan da ke tafe.
Tinubu ya gana da Jonathan a Abuja
Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci fadar Aso Rock Villa da ke Abuja domin ganawa da Shugaba Bola Tinubu.
Goodluck Jonathan ya kai ziyara fadar shugaban kasar ne da yammacin ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun shekarar 2026.
Ganawar dai na zuwa ne bayan Goodluck Jonathan ya kai irin wannan ziyarar a watan Nuwamban shekarar da ta gabata.
Asali: Legit.ng
