Ganduje Ya Karya Ministan Buhari, An Bar Wike Ya Samu Yadda Yake So a Jam’iyyar APC

Ganduje Ya Karya Ministan Buhari, An Bar Wike Ya Samu Yadda Yake So a Jam’iyyar APC

  • A karshe APC NWC ta tsige mutanen Rotimi Amaechi da su ke rike da shugabancin jam’iyyar APC a jihar Ribas
  • Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yarda Tony Okocha ya zama sabon shugaban rikon kwarya a Ribas da zai jagoranci APC
  • Abin da hakan ke nufi shi ne mutanen Nyesom Wike sun karbe APC, duk da Ministan bai bar jam’iyyar adawa ta PDP ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Rotimi Amaechi ya sake cin karo da cikas a tafiyar siyasa inda shugabannin APC na kasa su ka sauke shugabanninta na reshen Ribas.

Rahoton Daily Trust ya ce an yi waje da mutanen Rotimi Amaechi daga jam’iyyar APC, an kawo sababbin shugabannin rikon kwarya a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

‘Kuskuren’ da aka samu a takardun CTC ba ya nufin NNPP ta yi nasara a kotu, Lauya

Jam’iyyar APC
Shugaban APC a ofis Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Shugabannin rikon kwaryan da aka nada mutanen Nyesom Wike wanda yanzu haka shi ne Ministan harkokin Abuja, kuma jigo a jam’iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta hura wutan rikicin Amaechi v Wike

Shekaru kusan goma kenan ana rigimar siyasa tsakanin Nyesom Wike da tsohon ubangidansa watau Amaechi wanda ya yi minista kafinsa.

Amaechi ya sauka daga kujerar ministan sufuri bayan shekaru bakwai a gwamnatin Muhammadu Buhari domin neman tikitin shugaban kasa.

Tsohon gwamnan na Ribas bai samu takara a APC ba, tun daga nan aka ji labari ana zargin ya goyi bayan Atiku Abubakar a babban zaben 2023.

Shi kuma Wike wanda yanzu aka ba mutanensa mukamai a APC, ya goyi bayan Bola Tinubu.

Wike ya samu yadda yake so a APC Ribas

Cif Tony Okocha ne ya zama sabon shugaban rikon jam’iyyar APC na reshen Ribas, rahoton ya ce Cif Eric Nwibani kuma ya zama sakatarensa.

Kara karanta wannan

Kujera za ta haddasa sabuwar rigima tsakanin Wike da gwamnoni a Jam’iyyar PDP

Ragowar sun hada da Hon. Chibuike Ikenga, Prince Stephen Abolo, Hon. Silvester Vidin, Senibo Karibi Dan-Jumbo sai Miss Darling Amadi.

Okocha ya na cikin mutanen Wike wanda tun tuni yake neman APC NWC ta sauke mutanen Amaechi da ke rike da jam’iyyar a jihar Ribas.

Wannan mataki da APC NWC ta dauka a karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ba mutanen Wike damar da su ke nema a gida.

Wike: Ministan Abuja ya dage da aiki

Sabon Minista watau Nyesom Wike ya ce sun gabatar da kwarya-kwaryan kasafin kudi, kuma an ji labari Bola Tinubu zai aikawa majalisa.

Ma’aikatar Abuja za ta kashe N61bn kafin karshen shekarar 2024, saboda ayi wa ja jama’a ayyukan gadoji, tituna har da wuraren shakatawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel