Dangote Ya ba Surukinsa Dama, Ya Naɗa Shi Mukami Mai Gwabi a Kamfaninsa

Dangote Ya ba Surukinsa Dama, Ya Naɗa Shi Mukami Mai Gwabi a Kamfaninsa

  • An naɗa Jamil Mohammed Abubakar a matsayin Manajan darakta na sashen kayayyakin more rayuwa da sufuri a kamfanin Dangote
  • Jamil Mohammed Abubakar, shi ne surukin Aliko Dangote kuma naɗin na zuwa ne a cikin wani tsari na mika ragamar shugabanci ga ‘yan gida
  • Ana sa ran zai jagoranci faɗaɗa ayyukan tashoshin jiragen ruwa da hanyoyin kasuwanci a Najeriya da sauran ƙasashen nahiyar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos –Jamil Mohammed Abubakar, ƙwararre a fannin jiragen sama, ya samu sabon muƙami a kamfanin Dangote inda surukinsa, Aliko Dangote.

An naɗa shi a matsayin Manajan darakta na sashen kayayyakin more rayuwa da sufuri na kamfanin inda ake sa ran zai kawo sauye-sauye da dama.

Dangote ya ba surukinsa mukami a kamfaninsa
Alhaji Aliko Dangote, Jamil Mohammed Abubakar Hoto: Dangote Cement PLC/Jamil MD Abubakar
Source: Facebook

Business Insider Africa ta wallafa cewa wannan mataki na daga cikin jerin sauye-sauyen shugabanci da ke bai wa ‘yan uwa muhimmiyar rawa a cikin kamfanin da darajarsa ta kai Dala biliyan 33.

Kara karanta wannan

Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100

An yi sabon nadi a kamfanin Dangote

Rahoton ya ce naɗin, wanda ya fara aiki daga ranar 20 ga Afrilu, 2026, ya ba shi alhakin kula da tashoshin jiragen ruwa da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa da ke taimaka wa kasuwanci.

Wannan sashe na da matuƙar muhimmanci ga burin kamfanin na 2030, wanda ke nufin gina hanyoyin sufuri da kasuwanci a faɗin Afirka.

A wata sanarwa da ya aike wa ma’aikata, Dangote ya bayyana cewa Jamil Abubakar zai jagoranci ƙoƙarin buɗe sababbin hanyoyin kasuwanci da za su ƙarfafa fitar da kayayyaki da ci gaban masana’antu.

Haka kuma, zai riƙa kai rahoto kai tsaye ga shugaban kamfanin, tare da jagorantar faɗaɗa ayyuka a Najeriya da sauran ƙasashen nahiyar.

Kwarewar sabon jagora a kamfanin Dangote

A bangaren ƙwarewa, Jamil Mohammed Aubakar ya fara aikinsa a matsayin matukin jirgi kuma yana da sama da shekaru 14 yana aiki a fannin sufurin jiragen sama na kasuwanci.

Kara karanta wannan

Arewa da Kudu za su amfana da Tinubu ya nemi izinin sake ciyo bashin Dala miliyan 516

Ana sa ran surukin Dangote zai kara bunkasa kamfanin
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

Ya yi aiki a kamfanoni kamar IRS Airlines, Azman Air, NG Eagle da XE Jets, inda ya taɓa zama babban matuki a wasu daga cikin kamfanonin.

Baya ga ƙwarewarsa, yana da alaƙa mai ƙarfi da iyalan Dangote, domin ya auri Fatima Dangote, ‘yar autan shugaban rukunonin kamfanin, waccw ita ma babbar jami’a ce a kamfanin.

Manyan ‘yan siyasa da ‘yan kasuwne suka halarci aurensu a shekarar 2018, daga ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Haka kuma, Jamil Mohammed Abubakar ɗa ne ga tsohon Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar.

Matatar Dangote ta yi rangwame

A baya, mun wallafa cewa matatar man Dangote ta janye ƙarin ₦75 da ta yi a kan farashin da take sayar wa 'yan kasuwa litar fetur a Najeriya.

Faduwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, sakamakon tsagaita wutar Amurka da Iran, shi ne babban dalilin wannan rangwame da aka samu daga matatar.

Kara karanta wannan

"Kada ku bar Turawa su yaudare ku": Gumi ya shawarci gwamnati kan sulhu da ƴan ta'adda

Farashin ɗanyen man Brent ya sauka zuwa $94.76, yayin da man WTI ya ragu zuwa $97.88, lamarin da ya sa Dangote sauke farashinsa a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng