Bayan Yakin Iran, Dangote zai Kafa Sabuwar Dankareriyar Matatar Mai a Afrika
- Kasashen Kenya, Tanzania da makwabta na tattaunawa kan matatar hadin gwiwa yayin da Alhaji Aliko Dangote ya yi tayin ginawa a Afrika
- Dangote ya bayyana cewa a shirye yake ya gina matatar mai a Gabashin Afrika bayan barazanar man fetur da yakin Iran ya jefa kasashe
- Baya ga harkar makamashi, Aliko Dangote ya yi magana kan kafa masana'antar samar da taki, iya bukaci 'yan Afrika su zuba jari a gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tanzania - Kasashen Gabashin Afirka na tattaunawa kan shirye-shiryen gina matatar mai ta hadin gwiwa a tashar Tanga ta Tanzania, kamar yadda Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana a ranar Alhamis.
A halin yanzu, Gabashin Afirka na shigo da dukkan kayayyakin mai da aka tace daga waje, musamman daga Gabas ta Tsakiya, abin da ke sa yankin ya kasance cikin hadarin hauhawar farashi.

Kara karanta wannan
Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100

Source: Twitter
Rahoton Reuters ya nuna cewa kasashen yankin na fama da hauhawar farashin man fetur saboda matsalar da yakin Iran da Amurka ya haddasa a duniya.
Maganar Shugaban kasar Kenya
Yayin wan taro da aka yi a Nairobi na kasar Kenya, Shugaban kasa Willima Ruto ya bayyana cewa suna shirn ganin sun samar da matatar mai a Gabashin Afrika tare da hadin gwiwa da Dangote.
“Za mu gina matatar hadin gwiwa a Tanga domin amfaninmu baki daya, saboda za ta sarrafa man fetur daga Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Kenya, Sudan ta Kudu da kuma Uganda,”
In ji Ruto a wani sako da ya wallafa a X.
Maganar Dangote kan matatar mai
Attajirin Afirka, Aliko Dangote, wanda ya halarci taron, ya ce zai iya sake gina irin matatar da ya yi a Najeriya mai iya tace ganga 650,000 a rana a Gabashin Afirka, idan gwamnatocin yankin suka goyi bayan shirin.
“Alƙawarina a yau shi ne idan muka cimma matsaya da gwamnatoci uku ko hudu a nan, za mu jagoranci aikin kuma mu tabbatar an kammala matatar cikin shekaru hudu zuwa biyar masu zuwa,”
In ji Dangote.
Uganda ma ta ce tana shirin gina nata matatar, yayin da take fatan fara hakar mai a kasuwanci a bana. A shekarar 2024, ta sanar da wata yarjejeniya da kamfanin Alpha MBM domin gina matatar da za ta iya tace ganga 60,000 a rana.
Dangote ya kuma ce yana shirin kafa kusan masana’antun hada takin zamani guda 20 a fadin Afirka kafin shekarar 2028 domin biyan yawancin bukatun nahiyar.

Source: UGC
Dangane da shirin saka matatar sa a kasuwar hannayen jari, Dangote ya ce masu zuba jari na Afirka su shiga lamarin, yana mai cewa:
“Dukkan 'ya Afirka za su iya zuba jari. Zan rika biyan riba da Daloli.”
An kama barayi a matatar Dangote
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun sojin Najeriya sun kama wasu mutane da ake zargi sun shirya satar danyen mai a matatar Dangote.
An kama mutanen ne a kusa da wani waje da ruwa ke gudana, inda ake tura mai daga wajen zuwa matatar Dangote da ke jihar Legas.
Mutanen da aka cafke sun amsa laifinsu bayan kama su da kayayyakin da ake zaton suna amfani da su wajen aikata laifuffuka a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
