Gwamna Bala Ya Sauya Akalar Siyasarsa bayan Sanya Labule da Peter Obi
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sanya labule da tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi
- Bala Mohammed ya bayyana cewa ganawar tasu na da nasaba da neman hanyoyin samar da hadin kai da gina kasa
- Gwamnan ya kuma bayyana matsayar da ya dauka kan batun sauya sheka zuwa wata jam'iyyar siyasa da ake tunkarar zaben 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi magana bayan ya gana da tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi.
Gwamna Bala ya bayyana cewa yanzu shi "'dan siyasa ne mai zaman kansa" ba tare da tsayawa daram a kan kowace jam'iyyar siyasa ba.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Bala Mohammed ya yi wannan kalami ne yayin da ya karɓi bakuncin jiga-jigan jam'iyyar ADC, Peter Obi, tare da wasu masu ruwa da tsaki daga Kudu maso Gabas a Bauchi a ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Bayan sauya shekar Kwankwaso, wasu manyan jiga jigan siyasar Najeriya za su koma ADC
Wace jam'iyya Gwamna Bala zai shiga?
Gwamna Bala ya bayyana tattaunawar a matsayin wata ɓangare na shawarwari kan haɗin kan ƙasa da haɗin gwiwar siyasa.
“Babu PDP ko ADC da ke tsaye ita kaɗai. Ni 'dan siyasa ne mai zaman kansa yanzu, ita ma jam'iyyarsa tana cikin rashin tabbas. Mun zuba ido ga bangaren shari'a."
"Tabbas, dukkanmu muna cikin adawa ne, kuma shi ya sa na ce wannan tattaunawar siyasa ce. Ba za mu bayyana duk abin da muka tattauna ba dangane da matakan da muka ɗauka daki da daki."
- Gwamna Bala Mohammed
Me Gwamna Bala ya tattauna da Obi?
Gwamna Bala ya lura cewa tattaunawar da ake yi tsakanin 'yan siyasa na iya haifar da sababbin ƙasaitattun haɗaka gabanin zaɓubbuka masu zuwa.
“Ba za mu iya yin aiki ba tare da jam'iyya ba. A ƙarshe, yanayin siyasar yanzu ma yana iya taimaka mana mu haɗa kai tare da ƙarfafa damarmu ta cin zaɓe."
- Gwamna Bala Mohammed
Ya bayyana ziyarar ta Peter Obi a matsayin wata alama ta ƙoƙarin dinke rarrabuwar kawuna tsakanin shiyyoyi da kuma samar da haɗin kan ƙasa, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Source: Facebook
Jawabin Peter Obi da ya hadu da Bala
Tun da farko, Peter Obi ya ce ziyarar tana nufin samar da haɗin kai da ƙarfafa haɗin gwiwa a faɗin ƙasar.
“Manufar ita ce neman goyon baya da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki, musamman daga jihar Bauchi, a cikin burinmu na haɗa kan wannan ƙasa."
- Peter Obi
Peter Obi ya yi watsi da raɗe-raɗen sauya shekar siyasa, inda ya jaddada cewa taron ba batun siyasar jam'iyya ba ne.
“Ba muna kiran juna zuwa jam'iyyun siyasa ba ne; muna kiran kanmu ne domin gina Najeriya mafi kyau."
- Peter Obi
Gwamnan Bauchi ya fasa komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya hakura da komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Tattaunawar da aka gudanar tsakanin gwamnan da ɓangarensa na PDP da kuma shugabancin APC ta ƙare ba tare da cimma matsaya ba.
Fasa sauya shekar ya biyo bayan kin amincewar da jam’iyya mai mulki ta yi da tsarin 60-40 na ikon kula da tsarin jam’iyyar a jihar Bauchi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

