Sarki Ya Gina Shirgegen Masallaci, Ya Gayyaci Matar Tinubu, Fasto Oluremi Buɗewa

Sarki Ya Gina Shirgegen Masallaci, Ya Gayyaci Matar Tinubu, Fasto Oluremi Buɗewa

  • Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, tare da mataimakin gwamnan Lagos sun kaddamar da sabon babban masallaci
  • An gina masallacin ne a Odo Noforija a garin Epe wanda Sarki Babatunde Ogunlaja da Alhaji Abdul Jelili Animashaun suka gina
  • Jami’an gwamnati da manyan baki sun yabawa aikin, suna cewa hadin kai tsakanin Musulmi da Kiristoci alama ce ta zaman lafiya da ci gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lagos - Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta halarci bikin bude babban masallaci da wani basarake ya gina.

Oluremi ta samu halartar bikin ne tare da mataimakin gwamnan Lagos, Dakta Kadri Obafemi Hamzat yayin bude babban masallacin.

Oluremi Tinubu ta jagoranci bude masallaci
Manyan baki a bikin bude masallaci da matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu. Hoto: Epe News Post, Oluremi Tinubu.
Source: Facebook

Rahoton The Nation ya ce Sarkin Odo Noforija, Oba Babatunde Ogunlaja ne ya gina masallacin tare da shugaban kamfanin Al Hujaaj International Umrah da Hajj, Alhaji Abdul Jelili Animashaun.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Tinubu ya sanya labule da gwamnonin APC a Abuja

Oluremi Tinubu ta jagoranci bude babban masallaci

Sabon masallacin na dauke da kyawawan kayatattun abubuwa da kayataccen rubutun larabci a bango, da babban sashen salla mai bangaren maza da mata domin ibada.

An tsara shi ne domin daukar dimbin jama’a a lokacin sallar Juma’a da sauran tarukan addinin Musulunci a cikin al’umma.

Dakta Hamzat ya yabawa masu daukar nauyin aikin, musamman Sarkin da Alhaji Animashaun, yana cewa hadin gwiwarsu na nuna zaman lafiya tsakanin addinai.

Ya kara da cewa gina masallaci yana kawo lada daga Allah, tare da yabawa ruhin hadin kai da aka nuna wajen kammala wannan aiki mai muhimmanci.

Mataimakin gwamnan ya isar da sakon Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bakin mai taimaka mata kan harkokin jama’a, Wale Alawiye-King.

Ya ce Uwargidan shugaban kasa ta nuna farin ciki kan ci gaban da ake samu a Epe, tare da addu’ar ci gaba da bunkasa yankin baki daya.

Oluremi ta shawarci yan Najeriya kan zaman lafiya
Hoton matar Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Sen Oluremi Tinubu CON.
Source: Facebook

Tsohon gwamna ya bukaci hadin kan addinai

Kara karanta wannan

Arewa da Kudu za su amfana da Tinubu ya nemi izinin sake ciyo bashin Dala miliyan 516

Tsohon ministan ayyuka, Babatunde Fashola SAN, ya bayyana masallacin a matsayin alamar karfi ta hadin kai tsakanin mabiya addinai daban-daban a kasar nan.

Ya ce:

“Ba kawai bude masallaci muka zo yi ba; mun zo isar da sako na hadin kan addinai da kuma zaman lafiya a tsakanin al’umma.”

Ya kara da cewa hadin gwiwar Kiristoci da Musulmi wajen gina masallacin na nuna yadda bambancin addini zai iya karfafa ci gaban al’umma baki daya.

Fashola ya bayyana cewa asalin aikin ya samo tushe ne tun wani taron tunawa da mahaifinsa da aka gudanar a gidansa a ranar 5 ga Agusta, 2023.

Ya ce halartarsa wajen bude masallacin ya kara tabbatar da sakon hadin kai da wannan aiki ke dauke da shi ga al’umma.

Oluremi Tinubu ta tuno kalubale lokacin kamfe

A wani labarin, an ji cewa mai dakin Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu ta bayyana halin da ta shiga a lokacin da mai gidanta, Bola Tinubu ke neman mulkin Najeriya.

A cikin wani littafi da ta rubutu, ta bayyana cewa zaɓin takarar shugaban ƙasa da Tinubu ya yi a kan tikitin “Muslim‑Muslim” ya raba kan cocinta.

Oluremi Tinubu ta ce bakin jinin da wannan lamari ya jawo bai hana ta ci gaba da bauta wa Ubangijinta ba, har aka samu nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.