Mataimakin Sanusi a Bankin CBN Ya Fito Ya Soki Hukuncin Zaben Gwamnan Jihar Kano

Mataimakin Sanusi a Bankin CBN Ya Fito Ya Soki Hukuncin Zaben Gwamnan Jihar Kano

  • Kingsley Chiedu Moghalu ya yi magana a kan abubuwan da ke faruwa a kotu wajen yanke hukunci a kan zaben 2023
  • A jihar Kano an yi hukuncin da ya ja hankalin jama’a, tsohon ‘dan takaran shugaban kasan ya hango matsala a kasa
  • Moghalu ya ce wasu suna amfana da matsalolin da ake samu a wajen harkar shari’a da aikin gudanar da zabe a Najeriya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Da alama Kingsley Moghalu ya shiga sahun wadanda su ka yi Allah-wadai da hukuncin zaben gwamnan jihar Kano da aka yi.

A shafin Twitter, Kingsley Moghalu ya tofa albarkacin bakinsa game da abubuwan da ake ta fada a game da bangaren shari’a a Najeriya.

Kara karanta wannan

‘Kuskuren’ da aka samu a takardun CTC ba ya nufin NNPP ta yi nasara a kotu, Lauya

Kano.
Kingsley Moghalu da Muhammadu Sanusi II a Jihar Kano Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Tsohon mataimakin gwamnan na bankin CBN ya ce ana fuskantar barazana saboda abubuwa sun kama hanyar sukurkucewa a kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Moghalu wanda ya yi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar YPP bai ambaci Kano ba, amma rahoto ya zo mai nuna nan ya dosa.

Kano: Abin da Kingsley Moghalu ya fada

"Bangaren shari’a da hukumomin zabe suna tabarbarewa. Wannan ya na babban tasiri ga burinmu a kan damukaradiyya.
Mafi yawan lokuta, giyar amfanin da su ka samu ta na bugar da wadanda su ka ci moriyar matsalolin da aka samu a tsarin.
Amma tarihi ya nuna mana cewa nan gaba, hadarin hakan ba karami ba ne.

- Kingsley Chiedu Moghalu

An hau tituna saboda hukuncin zaben Kano

Can da zanga-zanga ta barke a Kano a kan hukuncin zaben, kwararren masanin tattalin arzikin wanda ya zama ‘dan siyasa ya sake magana.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Gobara ta yi barna yayin da wuta ta ci hukumar shari’a a jihar Kano

Moghalu ya nuna duk runtsin da aka shiga, bai kamata mutane su fita daga hayyacinsu ba, hakan na zuwa ne bayan rudani kan CTC.

"A yanayi na hayaniya da kwaratsi, dauke da yake-yake da rikici iri-iri, dole mu samu kwanciyar hankali ko a cikin kalubalen yau da gobe ne.
Mutum ne yake nemawa kan sa aminci. Mafi karfin mutane su ne masu samun kwanciyar hankali." - Kingsley Chiedu Moghalu

Ana ta zanga-zanga a Kano

Labari ya zo cewa Kwamishinan 'yan sandan Kano, Hussain Gumel ya ce wasu da su ka fita zanga-zanga a jiya sun shiga hannun hukuma.

Wasu sun fara zanga-zanga a Kano saboda tsige gwamna Abba Kabir Yusuf a kotu. CP Hussaini Gumel ya ce ba za su yarda da wannan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel