Mudathir Ishaq
18323 articles published since 08 Yun 2016
18323 articles published since 08 Yun 2016
Wannan ya zama wata manuniya dake nuni da cewa lallai 'yan ciranin da suka fito daga nahiyar Afrika zuwa kasar Amurka suna da kwazo da nagartar aiki, fiye da wadanda suka fito daga kasar Mexico da kuma nahiyar Amurka ta tsakiya
Duk da irin matsin lambar da yake samu daga bangarori daban-daban, da suka hada da danginsa, Shugaba Buhari yayi biris akan mayar da korarren shugaban hukumar jami'an tsaro ta farin kaya DSS, Lawan Daura a bakin aikinsa.
Matashin dan takarar shugaban kasa Omoyele Sowore ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta gaza cika alkawurran da ta daukan ma yan Najeriya, don hakan yake da yakinin zai kada shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba game da wannan sabuwar alaka da ake kokarin kullawa a tsakanin Jonathan da Kwankwaso, yau shekaru hudu kenan cif cif da Kwankwaso yayi gugar zana ga Jonathan da mabiyansa na jihar Kano.
Kungiyoyin fafutuka a jihar Nasarawa sun nuna damuwarsu kan yawaitar mambobin kungiyar Hakika a jihar da kuma yadda matasa ke shiga kungiyar. Wani masanin harkar tsaro, Dakta Nwani Aboko, ya laburta wannan abu ne a taron da kungiy
Gwamnatin kasar Saudiyya ta damke wani babban limamin haramin Makkah kuma Alkali a Makkah, Sheikh Dr. Saleh al Taleb, bayan ya gabatar da Huduba da ya soki sabuwar dokar halatta cakuduwan maza da mata a taro a kasar.
Duk da al'ummar kasar nan sun fi sabawa da mulkin zango biyu mai shekaru 4, amma kuma komai yana canzawa domin kuwa al'ummar ta canza, wanda hakan zai bayar da dama wajen yiwa kundin tsarin mulkin kasar nan kwaskwarima
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Kotun ta kama Zhu Xiaodong mai shekaru 31 da laifin kashe matarsa mai suna Yang Liping a shekarar 2016 bayan wata yar cacar baki data barke a tsakaninsu, sa’annan ya nannade gawar ta saka a cikin Firij.
Bayan wannan biki na nadin sarauta, jiga-jigan uku sun nufaci gidan shugaban kasa da misalin 2.40, inda rahotanni suka bayyana cewa sun kuma yi bankwana da gidan da misalin 3:35 na yammacin ranar Larabar da ta gabata.
Mudathir Ishaq
Samu kari