Basarake Ya Watsa Wa Pantami Kasa a Ido bayan Saka Shi Kwamitin Kamfen PDP
- Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zaben gwamna na 2027, amma Dagacin Herwagana ya yi watsi da nadin da aka yi masa
- Basaraen ya ce bai san da nadin mataimakin shugaban kwamitin hulda da manoma da makiyaya ba kafin ganin sunansa a jerin
- Basaraken ya bayyana cewa ba ya tare da kowace jam’iyyar siyasa, yana mai cewa a matsayinsa na jagoran gargajiya, al’ummar da yake jagoranta ba su da bambancin siyasa a wajensa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Pantami, Gombe - Jam'iyyar PDP a jihar Gombe ta fitar da jerin sunaye a kwamitin kamfen dinta na zaben gwamna a 2027.
Sai dai an samu akasi bayan saka sunan wani basarake da ke cikin birnin Gombe wanda ya yi watsi da nadin da aka yi masa.
Hakan na cikin wata sanarwa da Dagacin Herwagana, Alhaji Aminu Sulaimna Wuro Bokki ya firar a shafinsa na Facebook.
Basaraken ya nuna rashin jin dadinsa bayan saka shi a kwamitin kamfen inda ya ce shi ba dan siyasa ba ne.
Ya ce babu wanda ya tuntube shi game da nadin kuma a matsayinsa na jagoran al'umma a gargajiyance kowa na shi ne.
Sanarwar ta ce:
"Na samu labarin cewa sunana yana cikin jerin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP na jihar Gombe, inda aka sanya ni a matsayin mataimakin shugaban kwamitin hulda da manoma da makiyaya, al’amarin da ban da masaniya a kansa a baya.
"Ina son sanar da jama’a a hukumance cewa, a matsayina na mai rike da sarautar gargajiya (musamman, Dagacin unguwar Herwagana da ke Gombe), sannan kuma ma’aikacin gwamnati, ba ni da alaka da kowace jam’iyyar siyasa, kuma ba na shiga harkokin siyasar jihar Gombe.
"Saboda haka, ina daukar wannan nadin a matsayin ko dai wani yunkuri ne da aka yi da gangan ko kuma kuskure daga wadanda ke da alhakin sanya sunana cikin jerin kwamitin yakin neman zaben PDP. Don haka, ina bayyana kin amincewata da wannan nadin."
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng
