Shugaban INEC Ya Magantu kan Karɓar Muƙami bayan Barin Hukumar

Shugaban INEC Ya Magantu kan Karɓar Muƙami bayan Barin Hukumar

  • Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC, Joash Amupitan, ya ce ba zai karɓi wani mukamin siyasa ko diflomasiyya ba bayan kammala aikinsa
  • Amupitan ya bayyana hakan ne yayin wani taro a cibiyar Chatham House da ke Landan, inda aka tattauna batun zaɓen Najeriya na 2027
  • Ya kuma ce INEC ta ɗauki matakai domin inganta zaɓen 2027, ciki har da rage yawan masu zaɓe da kowace na’urar BVAS za ta tantance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi magana kan rayuwa bayan barin hukumar.

Amipitan ya bayyana cewa ba zai karɓi wani mukamin siyasa ko na diflomasiyya daga kowace gwamnati ba bayan kammala wa’adinsa a hukumar.

Shugaban INEC ya magantu kan rayuwa bayan kammala aikinsa
Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa da cibiyar Chatham House ta shirya a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027

Amupitan ya yi magana kan karɓar mukami

An tambayi shugaban INEC ko zai yi alkawarin ƙin karɓar wani mukamin siyasa ko diflomasiyya bayan barin hukumar, kamar yadda magabacinsa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi.

A watan Nuwambar shekarar 2025, Shugaba Bola Tinubu ya aika sunan Yakubu cikin jerin mutum 32 da ya zaɓa domin zama jakadu, daga bisani aka naɗa shi jakadan Najeriya marar aikin diflomasiyya a ƙasar Qatar.

Da yake amsa tambayar, Amupitan ya ce ba zai karɓi wani mukami daga hannun kowa ba saboda ya karɓi amanar al'umma ne domin gudanar da ayyukan zaɓe cikin adalci.

Ya ce:

“Ba zan karɓi wani mukami daga wurin kowa ba, domin zuwana wannan matsayi ya ginu ne bisa amana.
“Na kuma yi rantsuwar biyayya, ba wai kawai domin kasancewa mai tsaka-tsaki ba, har ma domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin 'yanci, adalci da sahihanci.”

Ya ƙara da cewa aikin INEC nauyi ne na ƙasa baki ɗaya, kuma ya kamata wanda ya yi hidimar jama'a tsawon lokaci ya samu damar kula da kansa.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ya tafi ƙasar waje, ya faɗa wa duniya matakin da za su ɗauka kan takarar Atiku a 2027

Matakan da INEC ke ɗauka gabanin zaɓen 2027

A wani ɓangare na jawabinsa, Amupitan ya yi magana kan yadda matsalolin da suka faru yayin zaɓen 2023 suka rage amincewar jama'a da hukumar INEC.

Ya bayyana cewa matsalar tattara da bayyana sakamakon zaɓe a Najeriya ba ta ta'allaka ga rumfunan zaɓe kawai ba, domin cibiyoyin tattara sakamako ma na da nasu ƙalubalen.

A cewarsa, matsalar da ta shafi aika sakamakon zaɓen 2023 ta faru ne saboda gazawar ɗora sakamakon a shafin tattara sakamakon zaɓe na IReV.

NDC ta zargi shirin maguɗin zaɓe

An ji cewa Seriake Dickson ya yi zargin cewa wasu na shirin sauya sakamakon zaɓen 2027 tare da amfani da jami’an tsaro na bogi wajen tsoratar da masu zaɓe.

Sanatan ya buƙaci INEC da jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu bisa doka, cikin adalci da ƙwarewa, tare da guje wa tsoratar da jama’a.

Dickson ya zargi APC da dogaro da taron jama’ar da aka biya kuɗi da kuma masu riƙe da muƙaman siyasa wajen nuna goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.