Babbar Magana: Kotu Ta Tsige Dan Takara a Jam'iyyar Su Kwankwaso, Ta Maye Gurbinsa
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige Hon. Onyeagucha Uchechukwu daga matsayin ɗan takarar sanatan jam’iyyar NDC a mazaɓar Imo ta Gabas
- Mai shari’a Mohammed Umar ya umarci jam’iyyar da INEC su amince da Uche Nwole a matsayin halastaccen ɗan takararta a zaɓen 2027
- Kotu ta ce Nwole ne ya lashe zaɓen fitar da gwani da INEC ta sanya ido a kai, don haka jam’iyyar ba za ta iya maye gurbinsa da ɗan takarar maslaha ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Mai shari’a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya tsige Hon. Onyeagucha Uchechukwu daga matsayin ɗan takarar sanatan jam’iyyar NDC a mazaɓar Imo ta Gabas da ke jihar Imo.
A maimakonsa, alƙalin ya umarci jam’iyyar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) su amince da Uche Nwole a matsayin halastaccen ɗan takarar NDC a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Shugaban INEC ba ya son a fitar da takardun Tinubu, ya shigar da bukata gaban kotu

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa a cikin hukuncin da ya yanke, kotun ta umarci INEC da ta gaggauta wallafa sunan Uche Nwole, kamar yadda ta yi wa ’yan takarar sauran jam’iyyun siyasa.
Dalilin tsige dan takarar NDC
Mai shari’a Umar ya ce kotun ta gamsu cewa mai ƙara, Nwole, shi ne ainihin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar, wanda INEC ta sanya ido a kansa yadda ya kamata.
Ya ce bisa tanade-tanaden Sashe na 84(1) da (2), da kuma Sashe na 86 na Dokar Zaɓe ta 2026, ya kamata NDC ta tsayar da sunan mai ƙara ta kuma aika shi ga hukumar zaɓe a matsayin ɗan takararta na sanata.
A cewar kotun, NDC ba za ta iya bisa doka ta tsayar da ɗan takarar maslaha wanda ba shi ne ya fito daga zaɓen fidda gwani da INEC ta sanya ido a kansa ba.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Kotu ta nemi shugaban INEC ya gabatar da takardun takarar Tinubu
Baya ga bayar da umarnin hana jam’iyyar har abada tsayar da wani suna ko aika wa INEC da sunan wani mutum a matsayin ɗan takara, kotun ta hana INEC karɓa, saka a jerinta ko wallafa sunan duk wani wanda ake ikirarin ya zama ɗan takarar NDC ta hanyar zaɓen fidda gwani da ba a taɓa gudanarwa ko sanya ido a kansa ba.
Haka kuma, ta hana hukumar amincewa da duk wani ɗan takarar maslaha wanda tsayar da shi ya saɓa wa Sashe na 87(1) da (3) na Dokar Zaɓe ta 2026.
Yadda Rikicin Ya Kaya
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1225/2026, inda NDC, INEC da Hon. Onyeagucha Uchechukwu su ne waɗanda ake ƙara na farko zuwa na uku.
Mai ƙarar ya yi zargin cewa duk da cewa shi ne ya samu mafi yawan sahihan ƙuri’u a zaɓen fidda gwani, jam’iyyar ta yi watsi da shi tare da zaɓar wanda ake ƙara na uku a matsayin ɗan takararta a zaɓen sanatan.
Mai shari’a Umar ya ce bayan nazarin dukkan shaidun da aka gabatar a gaban kotu, ya gamsu cewa ƙarar mai ƙara ta cancanci nasara. Saboda haka, ya amince da dukkan manyan buƙatu guda bakwai da ya gabatar.
Asali: Legit.ng