Tsautsayin Sallah: Hadari ya rutsa da wasu mutane 11, sun riga mu gidan gaskiya
- Kwana ya karewa wasu matafiya yayin tafiya don bikin Sallah
- Matafiyan suna kan hanyarsu ne ta Yuhuri zuwa Kontagora
- Bayan wadanda suka rasu, karin wasu sun jikkata an mika su asibiti
A kalla mutane goma sha daya ne suka rasu bisa wani hadarin mota da ya rutsa da su akan hanyarsu ta Yuhuri zuwa Kontagora dake jihar Niger.
Shugaban jami'an kiyaye hadura na yankin Kontagora Abdullahi Umar, ya tabbatarwa da menama labarai faruwar lamarin a jiya Laraba.

Ya kuma kara da cewa mutane 16 sun samu rauni, wanda yanzu haka suna babban asibitn garin Kontagora domin cigaba da karbar magani.
KU KARANTA: Aiyuka 4 da Buhari bai taba sanya mana baki ciki ba - Fashola
Jami’in ya shaidawa manema labarai cewa wata mota kirar Toyota ce tayi taho-mu-gamu da wata motar haya ta fasinjoji.
Umar ya gargadi masu abin hawa akan tukin ganganci da kuma gudun-wuce-sa'a.
Mutanen da lamarin ya rutsa da su dai an tabbatar da cewa sun taso ne daga garin Kontagora zuwa garin Yauri dake jihar Kebbi domin yin bikin sallah Babba.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng