Gwamna Ya Jero Dalilai 4 da Suka Sa Zai Yaƙi Tinubu a 2027 duk da Ya Goyi Bayansa a 2023
- Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana manyan dalilai hudu da suka sa ya yanke shawarar kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
- Ya ce matsalar tattalin arziki, yawan bayar da uzuri, raunin hadin kan kasa da rashin isasshen tallafi ga 'yan kasa ne suka jawo matakin nasa
- Makinde ya ce da shi ne shugaban kasa, da ya shirya matakan rage radadin cire tallafin man fetur kafin aiwatar da manufar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Shekaru uku bayan ya goyi bayan Shugaba Bola Tinubu a 2023, Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana dalilan da suka sa yanzu zai kalubalance shi a zaben 2027.
Gwamna Makinde, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na APM, ya lissafa manyan matsaloli guda hudu da yake ganin sun dabaibaye gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Bidiyon yadda aka tallafa wa Tinubu yana tafiya a wurin taro ya dauki hankali, Sowore ya yi magana

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya fitar ga yan Najeriya ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamba, 2026, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Gwamnan Oyo ya goyi bayan Tinubu a 2023
Makinde, ya ce matakin da ya dauka ba ya da nasaba da wata rashin jituwa ta kashin kai tsakaninsa da Tinubu ko kuma burinsa na zama shugaban kasa, sai dai damuwa ce kan makomar Najeriya.
Ya tuna cewa ya goyi bayan Tinubu ne saboda ya yi imanin cewa shugaban kasar zai iya hada kan 'yan Najeriya, kafa gwamnati bisa cancanta da kuma magance matsalolin tattalin arzikin kasar.
"Na goyi bayan Shugaba Tinubu a shekarar 2023 ne saboda na yi imanin cewa kwarewarsa da alakar siyasarsa za su taimaka masa wajen hada kan 'yan Najeriya," in ji Gwamna Makinde.
Dalilin Makinde na kalubalantar Tinubu
Dalili na farko da Makinde ya bayyana shi ne abin da ya kira "tabbatar da daidaiton tattalin arziki ba tare da samun ci gaban tattalin arziki ba".
Duk da amincewa da cewa an samu wasu sauye-sauye a wasu muhimman alkaluman tattalin arziki, gwamnan ya ce wadannan nasarori ba su haifar da ingantuwar rayuwar talakawan Najeriya ba.
Dalili na biyu shi ne abin da ya kira "mulki ta hanyar bayar da uzuri". Ya zargi gwamnatin da yawan jingina matsalolin da ake fuskanta ga gwamnatin da ta gabata, maimakon nuna ci gaba da za a iya aunawa wajen magance su.
"Kowace gwamnati tana gadon wasu matsaloli, amma ana zabar ta ne domin ta magance su," in ji shi
Dangane da hadin kan kasa, Makinde ya ce yana sa ran kwarewar Tinubu a siyasa da iya kulla kawance za su taimaka wajen kafa gwamnati da za ta hada kwararrun 'yan Najeriya daga sassa daban-daban.
Sai dai ya ce a maimakon haka, ya fara ganin cewa kawancen siyasarsa ya fi yi wa muradunsa na siyasa hidima fiye da muradun kasa.

Source: Twitter
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa dalili na hudu da ya bayyana shi ne "sauye-sauyen tattalin arziki ba tare da isasshen kariya ga 'yan Najeriya ba".
Duk da cewa ya goyi bayan matakan cire tallafi da tsarin canjin kudi Makinde ya ce ya kamata qgwamnati ta fara tanadar matakan kare 'yan kasa daga radadin da sauye-sauyen za su haifar kafin aiwatar da su.
Ya bayyana cewa miliyoyin 'yan Najeriya da tuni suke fama da matsin rayuwa sun kara shiga cikin wahala kafin gwamnati ta samar da isassun matakan tallafa musu.
Makinde ya ba yan Najeriya shawara
Kun ji cewa ɗan takarar shugaban kasa na APM, Gwamna Seyi Makinde, ya bukaci ‘yan Najeriya su karbi duk kudin da APC ta ba su a lokacin zaben 2027.
Gwamnan na jihar Oyo ya shawarci masu kada kuri’a su yi amfani da kudin, amma kada su hakan ya hana su zaben shugabanni nagari da za su kawo sauyi.
Asali: Legit.ng

