'Yan Bindiga Sun Jawo Wa Kansu Bala'i bayan Yunkurin Kai Hari a Katsina
- Rahotanni sun ce dakarun soji sun kashe aƙalla mutum 14 da ake zargin ’yan bindiga ne a wani artabu da ya faru a Gora
- Sojojin sun kuma ƙwato babura bakwai da ake zargin ’yan bindigar ke amfani da su wajen gudanar da hare-hare
- Nasarar da sojojin suka samu ta zo bayan hatsabiban 'yan bindigan sun shirya wani mummunan shiri a kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Rahotanni sun ce dakarun Sojojin Najeriya sun yi wa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne kwanton ɓauna ne a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe aƙalla 'yan bindigan 14 a Gora, da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Source: Twitter
Sojoji sun kashe 'yan bindiga
Jaridar The Punch ta ce lamarin ya faru ne a daren ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026, inda sojojin suka kuma ƙwato babura bakwai da ake zargin waɗanda suka mutu ke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
An bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da wasu ’yan bindiga da yawa suka yi yunƙurin kai wani hari a cikin al’ummar Gora da kewaye.
Wasu majiyoyi daga yankin sun shaida wa manema labarai a yammacin ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026 cewa maharan sun zo ne a kan babura, mutum biyu-biyu, ɗauke da muggan makamai.
Majiyoyin sun ce da farko ’yan bindigar sun yi yunƙurin yi wa jami’an sojoji kwanton ɓauna, amma dakarun sun riga sun san inda suke.
Sojoji sun yi wa ’yan bindigar kwanton ɓauna
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda dalilan tsaro ta ce sojojin sun kai wani samame na mayar da martani tsakanin al’ummomin Gora da Gidan Barau.
A cewarta, jami’an sojojin sun shirya musu kwanton ɓauna, wanda ya sa wasu daga cikin ’yan bindigar suka faɗa tarkonsu.
Majiyar ta ce bayan harin farko, wasu daga cikin ’yan bindigar sun yanke shawarar komawa wurin domin kwashe gawar ’yan uwansu da aka kashe.

Kara karanta wannan
Rashin imani: Yadda 'yan bindiga suka kona mutum 12 'yan gida 1 da ransu a Zamfara
Sai dai, a cewar majiyar, ba su san cewa sojojin sun sake shirya musu wani kwanton ɓauna a wurin ba.
"A ƙarshe, an kashe ’yan bindigar guda 14, yayin da dakarun sojoji suka ƙwato babura bakwai mallakinsu.” In ji majiyar.
An tabbatar da faruwar lamarin
Majiyoyin sun bayyana cewa kafin wannan lokaci, wasu yankunan karkara a ƙaramar hukumar Malumfashi na fuskantar hare-haren ’yan bindiga kusan kullum.
Sun ce maharan kan shiga ƙauyukan suna satar dabbobin gida tare da yin garkuwa da mutane.
Magajin garin Gora, Alhaji Gora, da wani mai riƙe da sarautar gargajiya a ƙaramar hukumar, Abdulaziz Sardauna, sun tabbatar da faruwar lamarin lokacin da aka tuntube su.
Sai dai, duk da tabbacin da shugabannin gargajiyar suka bayar, gwamnatin jihar Katsina, rundunar Sojin Najeriya da kuma rundunar ’yan sandan jihar ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Source: Original
'Yan bindiga sun kashe soja
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe soja, mafarauci da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Sarkin Yamma, kusa da yankin Jeb-Jeb da ke Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido ta Jihar Taraba.
Maharan wadanda ke dauke da makamai sun kuma harbi wani soja tare da jikkata shi, sannan suka yi awon gaba da wasu mazauna yankin zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng
