Ta tabbata: Buhari ba zai mayar da Lawan Daura shugabancin hukumar DSS ba

Ta tabbata: Buhari ba zai mayar da Lawan Daura shugabancin hukumar DSS ba

- Masu matsin lamba ga shugaban kasa akan mayar da Lawan Daura shugabancin hukumar tsaro ta DSS sun sha kasa

- Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya tsige Lawan Daura ba tare da sanar da Buhari ba, har sai daga baya

- Ana kan takaddamar wanda za'a nada sabon darakta janar na hukumar tsaro ta fararen kaya

Duk da irin matsin lambar da yake samu daga bangarori daban-daban, da suka hada da danginsa, Shugaba Buhari yayi biris akan mayar da korarren shugaban hukumar jami'an tsaro ta farin kaya DSS, Lawan Daura a bakin aikinsa.

A rahoton da Legit.ng ta samu, wasu daga cikin masu matsin lambar, sunbi sahun shugaban kasar har zuwa birnin Landan, inda suka bukaci ya mayar da Lawan Daura shugabancin hukumar, wanda mukaddashin shugaban kasa Osibanjo ya tsige.

A bangare daya kuwa, wadanda ke adawa da dawowar tsohon shugaban hukumar na ganim cewa Korar Lawan Daura wata babbar nasara ce a demokaradiya da kuma daga darajar gwamnatin Buhari.

Ta tabbata Buhari ba zai mayar da Lawan Daura shugabancin hukumar DSS ba
Ta tabbata Buhari ba zai mayar da Lawan Daura shugabancin hukumar DSS ba

Wannan tirka-tirka dai ta ci gaba da hauhawa, inda har lamarin ya kai gaban fadar shugaban kasar, musamman ma akan tunanin wanda zai maye gurbin tshon shugaban hukumar tsaron ta DSS.

KARANTA WANNAN: Buhari na samun matsin lamba akan mayar da Lawan Daura shugabancin hukumar DSS

Wasu na ganin dacewar damka shugabancin ga d'an Arewa. Wasu kuma na ganin dacewar amincewa da mai rikon kujerar darakta janar na hukumar a yanzu, Mathew Seiyefe, wanda tabbatar da shi zai sanya sabuwar soyayyar Buhari a idon 'yan kudu.

To sai dai takaddamar da ake yi akan Seiyefe na kara ruruwa, inda wasu ke ganin rashin dacewar bashi mukamin, ganin cewa shekara daya ce ta rage masa yayi ritaya. Ya kwashe shekaru 34 yana aikin gwamnati.

Wata majiya da tai magana da Legit.ng, ta ce: "Shugaban kasar ba shi da wani kudiri na Lawan Daura ya koma aiki, ya na da yakinin cewa wannan gwamnatin tana tafiya akan kaifi daya ne, don haka ba zai kalubalanci hukuncin da mataimakinsa yayi ba. Buhari mutum ne mai dattako."

Haka zalika, wata majiya daga fadar shugaban kasar ta yi tsokaci kan tsige Lawan Daura.

Majiyar ta ce: "Duk da cewa mataimakin shugaban kasa bai sanar da Buhari kudurin tsige Lawan Daura ba, har sai bayan da ya aikata hakan. Osinbajo ya sanar da shugaban kasa wannan kuduri daga baya, shi kuma shugaban kasa ya amince da hakan saboda fadar shugaban kasa na aiki a kaifi daya"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel