Tuna baya: idan mutum ya rasa madafa ko mai malfa ya gani sai ya bi shi – Kwankwaso

Tuna baya: idan mutum ya rasa madafa ko mai malfa ya gani sai ya bi shi – Kwankwaso

Masu iya magana suka ce baki shike yanke wuya, kuma dama duk abin dake baka tsoro, wata rana sai ya baka tausayi, wadannan maganganu biyu sun tabbata akan Sanatan Rabiu Kwankwaso da tsohon shugaban kasa Jonathan, a yayin da Sanatan ya kai ma Jonathan ziyara.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba, 22 ga watan Agusta ne tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya kai ma Gooluck Jonathan ziyara a gidansa don neman goyon baya tare da sa albarka a bukatarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019.

KU KARANTA: Mugunta ruwan fakko: Mutumin daya kashe matarsa ya gamu da fushin Kotu

Tuna baya: idan mutum ya rasa madafa ko mai malfa ya gani sai ya bi shi – Kwankwaso
Jonathan da Kwankwaso

Sai dai wani hanzari ba gudu ba game da wannan sabuwar alaka da ake kokarin kullawa a tsakanin Jonathan da Kwankwaso, yau shekaru hudu kenan cif cif da Kwankwaso yayi gugar zana ga Jonathan da mabiyansa na jihar Kano.

A cikin wani bidiyo da gidan talabijin na Dokin karfe ta fitar, an jiyo Kwankwaso yana shagube tare da yin hannunka ma sanda ga abokan hamayyarsa dake tare da Jonathan, inda yake cewa “idan mutum ya rasa madafa ko mai malfa ya gani sai ya bi shi”.

Kalli bidiyon:

amma abinka da siyasar bukatar son rai, sai ga Kwankwaso yau a gidan Jonathan yana neman kamun kafa, shin kodai Kwankwaso ya rasa madafa ne, ko kuwa ya manta ne?

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel