Zamfara: An Sanar da Sakamakon Zaben Fitar da Gwanin Dan Majalisar Tarayyar APC
- An sanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC a mazabar tarayya ta Kaura Namoda/Birnin Magaji da ke jihar Zamfara
- Aminu Sani Jaji, wanda shi ne dan majalisar wakilai mai wakiltar yankin, ya samu kuri'u 26,646
- An gudanar da sabon zaben ne bayan babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke nasarar Jaji a zaben farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Aminu Sani Jaji ya samu tikitin tsayawa takarar jam’iyyar APC a mazabar tarayya ta Kaura Namoda/Birnin Magaji da ke jihar Zamfara.
Hakan ya biyo bayan lashe sabon zaben fitar da gwani da aka gudanar ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026.

Source: Original
An sanar da sakamakon zaben fitar da gwani
Jaji, wanda shi ne dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar, ya samu kuri'u 26,646, inda ya doke sauran masu neman tikitin jam’iyyar guda biyu, cewar TVC News.
Shugaban kwamitin gudanar da zaben na APC, Kabiru Idris, ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara kuri'u da ke Kaura Namoda.
A sakamakon da kwamitin ya bayyana, Hassan Umar Dangaladima ya zo na biyu da kuri'u 713, yayin da Musa Zubairu bai samu ko da kuri'a daya ba.
Yadda Jaji ya samu nasara a mazabun biyu
Rahoton Punch ya nuna cewa mazabar tana da mambobin APC 42,266 da suka yi rajista, inda aka tantance masu kada kuri'a 27,389, sannan aka samu kuri'u 27,359.
A karamar hukumar Kaura Namoda, Jaji ya samu kuri'u 14,264, yayin da Dangaladima ya samu 465. Musa Zubairu bai samu kuri'a ko daya ba.
A bangaren karamar hukumar Birnin Magaji kuwa, Jaji ya samu kuri'u 12,382, yayin da Dangaladima ya samu kuri'u 248. Shi ma Zubairu bai samu kuri'a ba.
Bayan bayyana sakamakon, shugaban kwamitin zaben ya tabbatar da cewa Jaji ya cika dukkan sharuddan doka, kundin tsarin mulkin APC da ka'idojin zaben jam'iyyar.
Dalilin sake gudanar da zaben fitar da gwani
An gudanar da sabon zaben ne sakamakon karar da Dangaladima ya shigar a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda kotun ta soke tikitin takarar da APC ta bai wa Jaji a zaben farko.
Kotun ta kuma umarci jam'iyyar da ta sake gudanar da zaben fitar da gwani cikin makonni biyu.
Bayan hukuncin, shugabancin APC na kasa ya sanya ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, domin sake gudanar da zaben bisa umarnin kotun.
Nasarar Jaji a sabon zaben ta ba shi damar wakiltar APC a takarar kujerar mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji a zaben shekarar 2027.
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng

